✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya sallami shugabannin hukumomin sufurin Jiragen sama

Shugaba Tinubu ya nasa sabbin shugabanni a hukumomi shida da ke karkashin Ma'aikatar Sufurin Jiragen Sama

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya sallami shugabannin hukumomi shida da ke karkashin Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama

Hadimin Shugaban Kasa kan harkokin ada labarai, Ajuri Ngelale, ta sanar a daren Laraba cewa tinubu ta sallami shugabannin hukumomin ne domin ingantar harkar sufurin jiragen saman Najeria da kuma share hawaen matafiya.

Wadanda aka sallama sun hada da Shguaban Hukurmar Kula filaen jirgin sama (FAAN), Kabir Yusuf Mohammed da Shugaban Hukumar Sufurin Jiragen Sama (NCAA) Kafin Shuaibu Nuhu, da kuma Shugaban Kwalejin Koon ukun Jirgin Sama (NCA) Kafin Alkali Mahmud Modibbo.

Suran sune Shugaban Hukumar Kula da Sarafin Samaniya (NAMA), Tayib Adetunji Odunowo; Shugaban Hukumar Binciken Sufurin Jirage (NSIB), Akinola Olateru; da Shugaban Hukumar Hasashen Yanayi, Farfesa Mansur Bako Matazu.

Sabbin shugabannin hukumomin sufurin jiragen sama

Ajuri ya kara da cewa Tinubu ya nada sabbin shugabannin hukumomin kamar haka;

Sabuwar Manajana-Darkatan FAAN ita ce, Olubunmi Oluwaseun Kuku, sai Injiniya Umar Ahmed Farouk a matsayin sabon Manajan-Daraktan NAMA a yayin da Alex Badeh Jr. ya zama sabon Manajan-Darakan NSIB.

Farfesa Charles Anosike zai jagoranci NIMET, Kyaftin Chris Najomo zai jagoranci NCAA sai Josetp Shaka Imalighwe kuma NCAT  a matsayin mukaddasin shugaba.

Tinubu ya kuma ba wa ministan ma’aikatar, Festus Keyamo izinin kammala aikin daukar shugaban jami’ar tukin jiragen sama.