✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya sake zama shugaban ECOWAS

An sake zaɓensa a matsayin shugaban ECOWAS karo ma biyu cikin shekara guda.

An sake zaɓen Bola Ahmed Tinubu a matsayin Shugaban Ƙungiyar ECOWAS karo na biyu cikin shekara guda.

Sauran shugabannin ECOWAS, sun yanke shawarar sake zaɓarsa a taron ƙungiyar karo na 65 wanda ya gudana a fadar gwamnati da ke Abuja ranar Lahadi.

Tinubu zai kammala wa’adinsa na farko a ranar 9 ga watan Yuli, 2024.

Tinubu, cikin jawabinsa bayan sake zaɓarsa a matsayin shugaban ECOWAS, ya ce zai ci gaba da jan ragamar ƙungiyar domin kawo sauye-sauye masu alfanu.

“Na amince na ci gaba da jan ragamar shugabancin waɗannan maza da mata masu nagarta a wannan tafiya, domin inganta dimokuraɗiyyarmu da muka gada.”

A lokacin wa’adin Bola Ahmed Tinubu na farko, a matsayin Shugaban ECOWAS, an fuskanci juyin mulki a wasu ƙasashen mambobin ƙungiyar.

Hakan ya sanya ECOWAS ƙoƙarin ci gaba da dawo da Nijar, Mali, da Burkina Faso cikin ƙungiyar, bayan a baya sun bayyana ficewarsu daga cikinta.

Duk da ƙoƙarin ECOWAS, ƙasashen sun sake jaddada ƙudurinsu na ficewa daga cikinta.

Idan ba a manta ba, ƙasashe irin su Nijar, Burkina Faso da Mali sun fuskanci juyin mulki daga sojoji, waɗanda suka hamɓarar da gwamnatin fararen hula a ƙasashen.

Hakan ne ya sanya ECOWAS yin barazanar ɗaukar matakin soji musammam a Nijar matuƙar sojoji ba dawo da mulkin demokuraɗiyya a ƙasar ba.