✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya rattaba hannu kan dokar bai wa ɗalibai rancen kuɗin karatu

Wannan dokar ita ce irinta ta farko a tarihin Nijeriya da babu wanda zai gagara samun ilimi mai zurfi.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya rattaba hannu a kan dokar bai wa ɗalibai bashin karatu.

Ya sa hannu kan dokar ce a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a wannan Larabar.

Hakan na ƙunshe cikin wani saƙo da hadiminsa kan zaurukan sada zumunta, Dada Olusegun ya wallafa.

Dokar mai taken kudurin sauya wa dokar bai wa dalibai rancen karatu fasali ta 2024, an samar da ita ne domin kafa asusun tallafa wa ɗaliban makarantun gaba da sakandire.

A watan Nuwambar shekarar da ta wuce ne majalisar dokokin kasar ta amince da kudurin dokar, da ke neman kafa wata gidanauniyar da za ta riƙa ba daliban manyan makarantun kasar bashin kudin makaranta.

Sai dai ƙudirin ya fuskanci tasgaro dangane da wasu mas’aloli da suka shafi tsare-tsaren karɓa da biyan bashin kuɗin, lamarin da ya sanya Tinubu ya sake bitar ƙudirin tare da aike wa majalisa sabuwar buƙatar neman amincewarta.

A ranar 20 ga Maris, Majalisar Dattawa ta zartar da ƙudirin bayan nazarin rahoton kwamitinta da ke da alhakin kula da manyan makarantun da Asusun TETFUND da suka yi la’akari da kudirin.

Karkashin dokar bai wa ɗalibai rancen kuɗin karatu, za a ba da lamuni marar ruwa ga ’yan Najeriya da suka cancanci samun ilimi mai zurfi.

Masu ruwa da tsaki dai sun tabo batutuwan da suka shafi tsarin bayar da rancen kuɗin ga ɗalibai, musamman ma kan abin da ya shafi buƙatun cancanta, hanyoyin samar da kuɗaɗen, hanyoyin miƙa ɗalibai rancen da suka nema da kuma biyan bashin kuɗaɗen da sauran su.

Sabuwar dokar dai ita ce irinta ta farko a Najeriya a cewar Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila.

Gbajabiamila wanda shi ne ya kawo kudurin dokar lokacin yana kakakin majalisa, ya ce dokar za ta inganta kasar domin babu wani yaron Najeriya da za a hana wa damar samun ilmi mai zurfi saboda rashin kuɗi.