Shugaban Kasa Bola Tinubu, ya rattaba hannu a kan dokar da za ta bai wa daliban manyan makarantu bashi su yi karatu, su biya daga baya.
Mamba a rusasshen Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Dele Alake ne ya sanar da hakan ranar Litinin.
- Masarautar Zazzau ta soke hawan Babbar Sallah
- ’Yan Nijar sun fi mu jin haushin cire tallafin mai – Akpabio
Ya ce za a rika adana kudaden da za a yi amfani da su wajen aiwatar da shirin ne a lalitar Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, kuma za a rika bayar da su ne kawai ga daliban manyan makarantu masu karamin karfi.
Kudurin dokar dai, ainihi Kakakin Majalisar Wakilai ta tara, Femi Gbajabiamila ne ya gabatar da shi, kuma ya tsallake karatu na uku ne makonni biyu da suka gabata.
Dokar dai ta tanadi bayar da bashi mara ruwa ga daliban manyan makarantu marasa karfi ta hanyar Asusun Tallafa wa Ilimi na Najeriya.