Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun a matsayin mai riƙon muƙamin babban jojin Nijeriya.
Kekere-Ekun za ta zama Alƙalin Alƙalan Najeriya ta 23 idan har Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin nata.
- Ya shiga aikata laifuka domin tabbatar wa gwamnati yana raye
- Alƙalin Alƙalan Nijeriya Kayode Ariwoola ya yi ritaya
Sabuwar Alƙalin Alƙalan ta sha rantsuwar ce a zauren majalisa na Fadar Gwamnati da ke Abuja a ranar Juma’a.
Kekere-Ekun ta gaji Mai Shari’a Kayode Ariwoola wanda a ranar Alhamis ya yi ritaya bayan cikarsa shekaru 70 a doron ƙasa.
Shugaba Tinubu wanda ya dawo daga Faransa ya miƙa godiyarsa ga Ariwoola wanda ya fara aiki a matsayin Alƙalin Alƙalan Nijeriya a ranar 27 ga watan Yuni, 2022.
A ƙa’idar Kotun Ƙolin, babban alƙali mai biye da shi ne zai maye gurbinsa, wanda hakan ya sa Mai shari’a Kudirat ce za ta maye gurbin da zai bari.
Tun a ranar Alhamis ce Ajuri Ngelale, mashawarcin shugaban ƙasa na musamman kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, ya bayyana cewa Tinubu zai rantsar da Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun a matsayin sabuwar Alƙalin Alƙalan Najeriya (CJN).