Babban Hafsan Rundunar Sojin Kasa ta Nijeriya, Laftanar- Janar Taoreed Lagbaja, wanda ya zama shugaban rundunar a ranar 19 ga watan Yuni, 2023 ya rasu ne a ranar Talata bayan rashin lafiya.
Allah Ya yi masa rasuwa yana da shekaru 56, inda ya bar matarsa Mariya da ’ya’ya biyu.
Fadar Shugaban ƙasa ta sanar da rasuwar ta hannun Hadimin Shugaban ƙasa kan Yaɗa Labarai, Bayo Onanuga, yana mai miƙa ta’aziyyar Shugaba Bola Tinubu a ranar Laraba.
“Ya rasu ne dai a daren Talata a Legas bayan ya yi fama da rashin lafiya. An haifi Laftanar Janar Lagbaja a ranar 28 ga Fabrairun 1968. Ya zama Shugaban Hafsan Soji a ranar 19 ga Yuni, 2023.
Aikinsa na soja ya fara ne a lokacin da ya shiga makarantar horas da sojoji ta Nijeriya NDA a 1987.
A ranar 19 ga Satumbar 1992, aka ba shi muƙamin Laftanar na biyu a Rundunar Sojojin Nijeriya a matsayin mamba na kwas na 39 na yau da kullum.
A tsawon aikinsa, Laftanar Janar Lagbaja ya nuna kyakkyawan jagoranci da jajircewa, inda ya yi aiki a matsayin Kwamandan Runduna ta 93 da kuma bataliya ta musamman ta 72.
Ya taka rawar gani sosai a ayyukan tsaron cikin gida da dama da suka haɗa da ‘Operation Zaki’ a Jihar Benuwe da Lafiya Dole a Borno da Udoka a Kudu maso Gabashin Nijeriya da Operation Forest Sanity a Jihar Kaduna da Neja.
Tsohon ɗalibin Babbar Jami’ar Yaƙin Sojojin Amurka ne da ya samu digirin digirgir a fannin Ilimin Dabaru, inda ya nuna ƙwazonsa ga ci gaban ƙwarewa a shugabancin soja.
Shugaba Tinubu ya jajanta wa iyalansa da sojojin Nijeriya bisa wannan rashi.
Sanarwar ta zo ne bayan Shugaba Tinubu ya ɗaga likkafar Janar Olufemi Oluyede, wanda ya maye gurbin Lagbaja a matsayin muƙaddashinsa.