✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya kori Arabi, ya naɗa Pakistan a matsayin shugaban NAHCON

Tinubu ya kori Arabi yayin da EFCC ke gudanar da bincike a kansa game da aikin Hajjin 2024.

Shugaba Bola Tinubu, ya kori Jalal Arabi tare da naɗa Farfesa Abdullahi Saleh Usman Pakistan a matsayin sabon Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON).

Ajuri Ngelale, mai magana da yawun shugaban ƙasa ne, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, inda ya bayyana Farfesa Abdullahi Saleh Usman a matsayin sabon shugaban hukumar.

Ya ce Majalisar Dattawa za ta tabbatar da naɗin Usman a matsayin sabon shugaban hukumar.

“Farfesa Usman fitaccen malami ne, wanda ya samu shaidar kammala karatu daga Jami’o’i biyu na Musulunci – Jami’ar Madina da Jami’ar Peshawar ta Pakistan.

“Kazalika, ya ƙware wajen gudanar da aikin Hajji, bayan da ya taba riƙe muƙamin Shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Kano, kuma ya yi nasarar kula ayyukan Alhazai a ƙasar nan.

“Majalisar Dattawa za ta tabbatar da naɗin nasa. Shugaban na fatan sabon shugaban NAHCON ya yi aikinsa bisa gaskiya da riƙon amana ga ƙasa baki ɗaya.”

Arabi, wanda aka naɗa shugabancin hukumar a watan Oktoban 2023, ya samu matsala kan aikin Hajjin 2024, wanda gwamnatin tarayya ta bayar da tallafin Naira biliyan 90.

Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC), ta kama Arabi da sakataren hukumar, Abdullahi Kontagora kan zargin almundahana.

Majiyar EFCC ta ce an ƙwato kuɗi Riyal 314,098 na ƙasar Saudiyya daga hannun korarren shugaban na NAHCON.