Babban jagora a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya kai wa Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir ziyara a ranar Laraba.
Gwamnan Jihar, Aminu Bello Masari dua was manyan makarraban gwamnati a jihar na daga cikin tawagar da ta yi rakiyar Tinubu har fadar Sarkin da ke Kofar Soro.
- Tafiyar Hawainiya da Buhari ke yi ta yi yawa —Baba-Ahmed
- Dalilin da ba za a yi ‘zaben Kananan Hukumomi ba’ a Filato
- An tabbatar da Nababa a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Gidajen Yari
Daga fadar Sarkin, kai tsaye tawagar jagoran jam’iyyar ta kai ziyara Babbar Kasuwar Katsina inda ya yi jajen gobarar da ta lakume fiye da shaguna dari a ranar Litinin.
Tinubu ya ziyarci Jihar Katsina ne awanni kadan bayan fitar rahoton rashin kyakkyawar alakar da ke tsakaninsa da Shugaba Muhammadu Buhari.
Aminiya ta ruwaito cewa, al’amura sun dagule a tsakanin bangarorin biyu, inda a yanzu watanni 14 kenan ba su yi wani zama karkashin rufi daya ba sabanin yadda ta kasance a baya.
Duk da cewa har kawo yanzu Tinubu bai fito karara ya bayyana sha’awarsa ta tsayawa takarar kujerar shugaban kasar ba, sai dai alamu sun nuna cewa yana ci gaba da kokarin cin gajiyar Buhari.
Wani daga cikin dangin Buhari a zantawarsa da Aminiya ya ce, ana kokarin shawo kan Shugaban Kasar don ganin ya goyi bayan dan takarar da zai kare muradinsa idan ya sauka daga mulki a 2023.
“Mun lura cewa Tinubu ba zai iya kiyaye muradin Buhari ba bayan ya sauka daga mulki, saboda haka yanzu wata mafitar ake nema domin cimma burinmu.”
“Muna kokarin shawo kan Shugaban ya goyi bayan dan takarar da zai kare muradinsa bayan cikar wa’adinsa a kujerar mulki,” a cewar majiyar wacce ta nemi a sakata sunanta.