Shugaba Bola Tinubu ya mika saƙon jaje da ta’aziyya ga Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, kan mutuwar mutane 17 da wani matashi ya cinna musu wuta suna tsaka da sallar asuba a makon da ya gabata.
Lamarin dai ya faru ne a garin Larabar Abasawa da ke karamar hukumar Gezawa, kuma tuni aka gurfanar da matashin a gaban Babbar Kotun Shariar Musulunci da ke Rijiyar Zaki.
- Hayaƙin janareta ya kashe dalibai 7 a Bayelsa
- Majalisar Kano za ta yi wa dokar masaratu gyaran fuska
Alkalin kotun, Mai Sharia Halhalatulhuza’i Zakariyya, dai ya bayar da umarnin tsare matashin a gidan yari bayan ya amsa laifinsa, sannan ya dage sauraren shari’ar zuwa ranar 31 ga watan Mayu, 2024.
A sanarwar da mashawarcin shugaban a bangaren watsa labarai, Ajuri Ngelale ya fitar, Tinubu ya yi tir da lamarin, tare da bai wa jami’an tsaron jihar umarnin gudanar da bincike, domin matashin ya girbi abin da ya shuka.
Haka kuma ya yi wa sauran wadanda lamarin ya rutsa da su da ke kwance a asibiti fatan samun lafiya, tare da jajanta wa al’ummar jihar da duk waɗanda abun ya shafa.