✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya isa majalisa don gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2025

Tinubu zai kasafin kuɗin na 2025 ga ’yan majalisa don yin nazari.

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya isa Majalisar Tarayya da ke Abuja, domin gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2025.

Kasafin kuɗin, wanda ya kai Naira tiriliyan 47.96, Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC), ta amince da shi kuma yanzu za a gabatar da shi ga ’yan majalisa don yin nazari.

Shugaban ƙasa ya isa zauren Majalisar Wakilai tare da ministoci, masu ba shi shawara, da sauran manyan jami’an gwamnati, tare da jami’an tsaro.

A ranar 19 ga watan Nuwamba, 2024, Tinubu ya aike tsarin kashe kuɗaɗe (MTEF) da takardar dabarun kuɗi (FSP) na 2025 zuwa 2027 ga Majalisar Tarayya.

’Yan majalisar sun amince da tsarin, kuma ana sa ran gabatar da shi a zauren majalisar a yau.

Tsarin ya ƙunshi farashin canjin dala ɗaya a kan Naira 1,400, tare da farashin man fetur da aka sa a kan dala 75 da 76.2 da kuma 75.3 kan kowace ganga.

Haka kuma, an yi ƙiyasin za ake fitar da ɗanyen mai ganga miliyan 2.06 da miliyan 2.10 da miliyan 2.35 a kowace rana a cikin shekarun.