Kungiyar da ke fafutuka wajen tabbattar da takarar Bola Ahmad Tinubu a matsayin Shugaban kasa a karkashin tutar jam’iyyar APC ta ce babu wanda ya fi gwaninsu cancanta ya mulki Najeriya.
Kungiyar, mai taken Tinubu Support Organization (TSO) bangaren mata ta kuma yi kira ga matan Jihar Kano da su goya wa dan takararsu baya don ganin ya ciyar da kasar nan gaba.
Shugabar da ke kula da bangaren wayar da kan mata a yankin Arewa maso Yamma, Hajiya Hauwa Shehu Tahir ita ce ta yi wannan kira a wani gangami da ta shirya don wayar da kan matan Jihar game da takarar Ahmad Bola Tinubu.
Hajiya Hauwa ta ce TSO karkashin jagorancin Daraktanta, Janar Aminu Suleiman tana kokarin wayar wa matan Arewa kai game da cancantar Bola Ahmad Tinubu a matsayin Shugaban kasa a zaben shekarar 2023.
Hajiya Hauwa ta kara da cewa duk a cikin ’yan takarar kujerar Shugabancin Kasar nan babu dan takarar da ya fi Tinubu cancanta da kujera duba da yadda ya gyara Jihar Legas a shekaru takwas da ya mulki Jihar.
“Ba wai kawai muna fadi a zabi Tinubu don muna son sa kawai ba, muna yin hakan ne don mun san ya cancanci ya rike wannan kujera. Duk wanda ya san Jihar Legas a baya na tabbata shi shaida ne game da irin kokarin da Tinubu ya yi wajen gyara Jihar . To irin wannan romon dimukuradiyyar muke so mu sharba a fadin kasar nan. Muna so Najeriya ta zama kamar Dubai ”
Ta kuma yi kira ga dukkan matan Arewa da su fito su zabi Bola Ahmad tinubu dan ci gaban rayuwarsu.
A nasa jawabin Darakta Janar na Kungiyar Tinubu Support Organization Honorabil Aminu Suleiman ya bayyana cewa sun tattauna da matan ne don sanin muhimmanci mata a tafiyar siyasa inda ya yi alkawarin ganin cewa an yi tafiya da matan ba tare da barin su a baya ba.
“Mata ku ne iyayenmu. A duk lokacin da ake maganar zabe ana maganar mata. Akwai mazajenku da yayanku Muna kira gare ku da ku yi amfani da kuriarku da ta iyalanku wajen zaben dan takarar da zai kawo muku ci gaba a rayuwarku Amma ba wanda zai sayi kuriarku ya gudu ya ki yi muku aiki ba.”
“Mun tabbatar idan kuka zabi Bola Ahmad Tinubu ba za ku yi da na sani ba domin zai kawo muku ci gaban da za ku dade kuna mora har zuwa jikokinku.”
Ya kuma yi kira ga matan da su yi fitar farin dango domin su karbi rajistar zabe.
“Duk yadda kike son Bola Tinubu idan ba ki da kuria to a ranar zabe ba za ki iya zabensa ba sai dai ki zama yar kallo.
“Don haka Ina kira ga duk wadanda ba su karbi rajistar ba da su hanzarta su karba. Idan za ku tafi ku hadu da dukkanin yayanku da suka kai shekaru sha takwas da haihuwa domin su ma su karbi tasu,” inji Hajiya Hauwa.
Matan da suka halarci taron wadanda suka fito daga Kananan Hukumomin Jihar 44 sun nuna jin dadinsu game da haduwarsu da Shugabannin inda suka ce a yanzu sun kara samun wayewa game da tafiyar, inda suka sha alwashin zaben wanda ya cancanta.