✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya fara shirin sauke wasu ministocinsa

Yanzu kallo ya koma kan Tinubu na ganin ministocin da zai sauke daga muƙamansu.

Shugaba Bola Tinubu, ya jagoranci taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) yau a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, yayin da ake ci gaba da raɗe-raɗin cewar zai sauke wasu ministocinsa.

Rahotanni da dama sun nuna cewa Tinubu na shirin yin wasu sauye-sauye nan ba da jimawa ba, bayan ya yi barazanar sallamar wasu ministocinsa da ba su taka rawar gani ba.

Duk da haka, shugaban ƙasar bai tabbatar da takamaiman lokaci ko yadda sauyin zai kasance ba.

A taron majalisar, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya jinjina wa Tinubu kan rawar da ya taka wajen tabbatar da sahihin zaɓe a Jihar Edo.

Ya kuma taya jam’iyyar APC, murna kan nasarar da suka samu a zaɓen Sanata da aka gudanar kwanan nan a jihar.

Akume, ya kuma sanar da majalisar game da rasuwar tsohuwar Ministar Harkokin Mata, Salome Jankada, wadda ta rasu a ranar 27 ga watan Agusta.

Majalisar ta yi ta’aziyya tare da girmamawa ga tsohuwar ministar.

Manyan jami’an gwamnati irin su Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkar Tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, da wasu ministoci sun halarci taron.

Sai dai hankali ya karkata kan yiwuwar Tinubu na sauya ministocinsa a nan gaba kaɗan.