✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya dawo bayan kwana 12 a Birtaniya

Oshiomhole da abokin takarar Tinubu, tsohon gwamnan Jihar Borno, Kashim Shetttima sun tarbe shi a filin jirgi

Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC a zaben 2023, Bola Tinubu, ya dawo Najeriya bayan shafe kwana 12 a kasar Birtaniya.

Hadimin Shugaban Kasa kan Kafofin Yada Labarai na Zamani, Bashir na daga cikin wadanda suka fara sanar da dawowar tasa a yammacin ranar Alhamis.

A bidiyon dawowar Tinubun da ya wallafa a shafinsa, Bashir Ahmad ya ce, “Dan takararmu na shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu ya dawo Najeriya daga London.”

A cikin bidiyon, abokin takarar Tinubu, tsohon gwamnan Jihar Borno, Kashim Shetttima ya tarbe shi a filin jirgi na Murtala Mohammed da ke Legas.

Tsohon Gwamnan Jihar Edo kuma tsohon Shugaban APC na Kasa, Adams Oshiomhole ke cikin wadanda suka tarbe shi.

Tafiyar Tinubu Birtaniya a baya-bayan nan ta tayar da kura, musamman bayan fitar wadansu bidiyonsa yana tsaka da motsa jiki.