Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC a zaben 2023, Bola Tinubu, ya dawo Najeriya bayan shafe kwana 12 a kasar Birtaniya.
Hadimin Shugaban Kasa kan Kafofin Yada Labarai na Zamani, Bashir na daga cikin wadanda suka fara sanar da dawowar tasa a yammacin ranar Alhamis.
- Fasinjojin Jirgin Kasa Sun Hadu da Iyalansu
- Ranar Juma’a kotu za ta yanke hukunci kan karar da ASUU ta daukaka
A bidiyon dawowar Tinubun da ya wallafa a shafinsa, Bashir Ahmad ya ce, “Dan takararmu na shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu ya dawo Najeriya daga London.”
A cikin bidiyon, abokin takarar Tinubu, tsohon gwamnan Jihar Borno, Kashim Shetttima ya tarbe shi a filin jirgi na Murtala Mohammed da ke Legas.
Tsohon Gwamnan Jihar Edo kuma tsohon Shugaban APC na Kasa, Adams Oshiomhole ke cikin wadanda suka tarbe shi.
Tafiyar Tinubu Birtaniya a baya-bayan nan ta tayar da kura, musamman bayan fitar wadansu bidiyonsa yana tsaka da motsa jiki.