Sakamakon zaben Shugaban kasa da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana a Jihar Oyo ya nuna cewa Bola Ahmed Tinubu na Jam’iyyar APC ne ya yi nasara da yawan kuri’u 312,449
Hukumar ta bayyana cewa dan takarar babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar, ya zo a matsayi na biyu da kuri’u 130,970, sai Peter Obi na LP ya zo na uku ne da kuri’u 68,302.
Sakamkon zaben da Baturen zaben, Babatunde Olusola Kehinde, ya sanar ya nuna Tinubu ya lashe daukacin kananan hukumomin jihar guda 33.
Haka kuma Jam’iyar ta APC ce tayi nasarar lashe duka kujeru uku na Majalisar Dattijai a Jihar ta Oyo kamar yadda Hukumar zabe INEC ta bayyana.
A mazabar Oyo ta Kudu, Cif Sharafadeen Ali na Jam’iyar APC ne ya yi nasara da kuri’u 111,513 a yayin da Cif Joseph Tegbe na Jam’iyar PDP ya zo na biyu da kuri’u 92,481 da Cif Kola Kola-Daisi na Jam’iyar ACCORD ya zo na uku da kuri’u 33,641.
A Oyo ta Arewa, Sanata Buhari Abdulfatai na APC da ke kan gado ne yayi nasarar ta-zarce da kuri’u 90,078, Mista Akinwale Akinwole na PDP yake biye da kuri’u 77,034, sai Cif Shina Peller na Jam’iyar ACCORD da ya zo na uku da kuri’u 54,732.
A mazabar Oyo ta Tsakiya, Dokta Yunus Abiodun Akintunde na APC ne ya yi nasara da kuri’u 108,776, Cif Oyebisi Ilaka na PDP ya zo na biyu da kuri’u 101,213.