✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya bai wa jihohi N108bn domin magance matsalar ambaliyar ruwa

Tinubu ya nuna himmarsa ta haɗa hannu da jihohi domin magance irin waɗannan matsalolin.

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya amince da bai wa jihohi 36 na ƙasar naira biliyan 108 domin su shawo kan matsalar ambaliyar ruwa.

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a fadar gwamnati da ke Abuja, babban birnin kasar.

Da yake karɓar Shugaban Majalisar Wakilai Abbas Tajudeen, mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana halin da ake ciki a Maiduguri a matsayin wani iftila’i da ya shafi ƙasar.

Shettima ya ce “Shugaba ƙasar ya nuna himmarsa ta haɗa hannu da jihohi domin magance irin waɗannan matsalolin.

“Kwanan nan, ya [Tinubu] amince da a saki Naira biliyan 3 ga kowace jiha domin magance wasu ƙalubalen da ake fuskanta ta yadda dukkan sassan tarayya su samu saye da kuma mallakar abubuwan da suke buƙata.”

Shettima ya kuma yaba wa shugaban majalisar bisa abin da ya bayyana a matsayin “jagorancinsa a majalisar dokokin kasar,” yana mai cewa duk da cewa an rantsar da kusan kashi 70 cikin 100 na ‘yan majalisar a matsayin sababbin ‘yan majalisa, shugaban majalisar, ya samu damar ci gaba yin jagoranci nagari.

“Akwai kwanciyar hankali sosai a Majalisar Wakilai, kuma dole ne mu yaba muku da samar da wannan shugabanci.

“Muna yi muku fatan alheri, kuma Insha Allahu kuna ɗaya daga cikin jiga-jigan tafiyar dimokuraɗiyyarmu.

“Dangantakar da ke tsakanin ɓangaren zartarwa, majalisa da kuma ɓangaren shari’a na da matuƙar muhimmanci wajen ɗorewar dimokraɗiyya a Najeriya.

“Har wa yau, na gode ƙwarai a madadin shugaban ƙasa, gwamnati da jama’ar Borno bisa yadda kuka nuna tausayi da goyon baya,” in ji shi.

A nasa ɓangaren, Abbas Tajuddeen ya jajanta wa Shettima da Tinubu da gwamnati da al’ummar Jihar Borno, inda ya ba da tabbacin cewa majalisun tarayya za su samar da tallafi ga al’ummomin da ambaliyar ta shafa.

“In sha Allah komai zai wuce kuma mutane za su koma garuruwansu, su ci gaba da rayuwarsu kamar yadda suka saba kamar babu abun da ya faru.

“Don Allah ka isar mana da saƙonmu na jaje zuwa ga gwamna da al’ummar Borno,” inji shi.