Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari, ya ce dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya bai wa iyalan wadanda ’yan bindiga suka kashe a jihar kyautar Naira miliyan 100.
Masari ya bayyana haka ne a taron yakin neman zaben Tinubu a Katsina, inda ya ce gwamnatinsa na kokarin kawo karshen matsalar rashin tsaro a jihar.
- Canjin kudi da wahalar mai sun kai ’yan Najeriya bango
- Wadanda suka rasu a girgizar kasar Turkiyya da Syria za su kai 20,000 —Jami’an lafiya
A cewarsa, dan takarar ya bayar da kyautar kudin don rabawa iyalan wadanda ’yan bindiga suka kashe sannan ya yi addu’ar Allah Ya jikan mutum 40 da ’yan bindiga suka kashe a jihar a makon da ya wuce.
Masari ya ce, “Shugabanci ba abun wasa ba ne, yana bukatar jajirtattun mutane; Idan ka yi wasa da shugabanci na lokaci kalilan, to za a shafe shekaru ana shan wahala.”
A cewarsa, da gwamnatocin baya sun yi abin da ya dace yanzu ba a samu ’yan ta’adda irin Boko Haram ba.
Don haka ya bukaci ‘yan Najeriya da kada su yarda wani ya fake da matsalar talauci da rashin tsaro wajen neman kuri’arsu.