Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa Tsohon Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Attahiru Muhammadu Jega, a matsayin Mashawarci kuma Mai Kula da Shirin Gyaran Noma da Kiwo na Shugaban Ƙasa.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ne, ya tabbatar da naɗin cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.
Shugaba Tinubu na fatan wannan naɗi zai kawo ci gaba a harkar noma da kiwo, tare da ƙarfafa yunƙurin raya ƙasa.
Farfesa Jega, wanda tsohon Shugaban Jami’ar Bayero ta Kano ne, ya kasance mataimakin shugaban Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Gyaran Noma da Kiwo tare da Shugaba Tinubu.
Kwamitin ya gabatar da shawarwari masu muhimmanci kan yadda za a inganta harkar noma da kiwo, ciki har da ƙirƙirar Ma’aikatar Kiwo, wacce yanzu haka ta ke da minista.
Jega mai shekara 68 a duniya, yana da ƙwarewa sosai a fannin shugabanci.
Yana cikin Kwamitin Shawara na Ƙasa da Ƙasa kan Zaɓe kuma shi ne Shugaban Majalisar Gudanarwa na Jami’ar Ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke Kano.
Ya shugabanci INEC daga shekarar 2010 zuwa 2015, inda ya jagoranci ayyukan zaɓe a Najeriya a wannan lokaci.
A cikin sanarwarsa, Onanuga ya bayyana cewa naɗin Jega a matsayin mashawarci na musamman zai taimaka wajen ci gaba da aiwatar da shirin gyaran noma da kiwo da kuma tabbatar da nasarorin da aka riga aka samu.