Jagoran jam’iyyar APC na kasa Bola Ahmed Tinubu ya ja hankalin masu zanga-zangar #EndSARS da su bawa gwamnati dama domin yin duba tare da magance korafe-korafensu.
Kusan mako biyu ke nan matasa na da zanga-zanga dangane da zaluncin da kuma karya dokar hakkin dan adam da jami’an ’yan sandan runsunar SARS da aka rusa ke yi.
- An kaddamar da shirin tallafin N75bn domin matasa
- ’Yan daba sun tarwatsa zanga-zangar #EndSARS a Kano
- Yadda aka kama barawon waya a zanga-zangar #EndSARS
“Da farko zanga-zangar ta fi mai da hankali ne a kan rukunin jami’an SARS, masu yaki da ayyukan fashi da kuma manyan laifuka.
“Amma daga bisani sai ta dauki salo na daban, inda wasu bangarori suke son a sauya fasalin rundunar ’yan sandan kasar nan, wasu kuma na son a hukunta dukkannin wani jami’in SARS da ake tuhuma da laifin cin zarafin al’umma.
“Har wa yau, wasu yankuna na kasar nan musamman, Arewancin kasar nan su ma sun fito domin yin tasu zanga-zangar domin kawo karshen matsalar ayyukan ’yan Boko Haram, masu garkuwa da mutane, rikicin makiyaya da manoma da ta’addacin ’yan bindiga da suka addabi yankin tsawon shekaru”, inji shi.
Sai dai a ranar Litinin Tinubu ya bayyana cewa babu wata gwamnati da za ta tsinci kanta a irin wannan hali a ce ba za ta saurari koken al’ummarta ba.
“Ba zai taba yiwuwa mutum mai hankali da ke martaba doka da dimokuradiyya ya ki saurarar koken masu zanga-zangar nan ba.
“Sai dai yana da kyau masu zanga-zangar #EndSARS su ba wa gwamnati dama domin yin gyara a kan harkar tsaro.
“Dole gwamnati ta yi gyara tare da cika alkawuran da ta dauka kuma ina da yakinin za a samu wannan gyaran”, cewar Tinubu.
Tinubu ya kara da cewa, in har masu zanga-zangar suka sauya akalar zanga-zangar ta zaman a sauyin gwamnati kamar yadda hakan ta faru a wasu yankuna, to,tabbas gwamnati ba ta da wani zabi da ya wuce ta yi amfani da doka domin wanzar da zaman lafiya.