Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya dage gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2025 ga Majalisar Tarayya zuwa ranar Laraba, 18 ga watan Disamba, 2024.
Wannan na zuwa ne bayan taron Majalisar Zartaswa ta Tarayya, kamar yadda Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris, ya tabbatar.
- ’Yan sanda sun kama ɓarayi 2, sun ƙwato wayoyi 25 a Borno
- Abba ya miƙa sunayen sabbin kwamishinoni ga majalisar dokokin Kano
“An ɗage gabatar da kasafin kuɗin shugaban ƙasa zuwa ranar Laraba saboda wasu muhawara da ake yi,” in ji Idris.
Tun da farko, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya sanar cewa za a gabatar da kasafin kuɗin a ranar Talata, 17 ga watan Disamba, 2024, a zauren Majalisar Wakilai.
Sai dai daga baya wasu majiyoyi daga Majalisar Tarayya, sun bayyana cewa an ɗage gabatar da kasafin, ba tare da bayani ba.
Wani ɗan majalisa ya ce, “An ɗage gabatar da kasafin kuɗin na Naira tiriliyan 47.9 na shekarar 2025 da Shugaba Tinubu zai yi zuwa ranar Laraba.”
Shirye-shiryen tarbar shugaban ƙasa sun kammala, inda aka girke jami’an tsaro a wajen harabar majalisar.