✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya ƙirƙiro ma’aikatar harkokin kiwon dabbobi

Tinubu ya ƙirƙiro da ma’aikatar domin magance rikice-rikicen noma da makiyaya.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya kafa sabuwar Ma’aikatar Harkar Kiwon Dabbobi.

Ya sanar da hakan ne lokacin da ya ƙaddamar da kwamitin da zai gyara tsarin kiwo.

Kwamitin zai yi aiki wajen magance matsaloli tsakanin manoma da makiyaya.

A taron, mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume da shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, da wasu jami’an gwamnati na daga cikin waɗanda suka halarci taron.

A watan Satumban 2023, Shugaba Tinubu ya amince da kafa kwamitin shugaban ƙasa don gyaran ɓangaren kiwo da magance rikice-rikicen makiyaya da manoma.

Wannan shawarar ta biyo bayan rahoton taron ƙasa kan gyara tsarin kiwo da rage rikice-rikicen da ke da nasaba da kiwo a Najeriya.

Kungiyar Miyetti Allah ta MACBAN, ta buƙace shugaban ƙasa ya ƙirƙiro ma’aikatar kiwo.

Shugabansu, Alhaji Baba Usman Ngelzarma, ya ce makiyaya na buƙatar ma’aikata mai zaman kanta da za ta kula da dukkanin al’amuran da suka shafi kiwo.

Ngelzarma ya bayyana cewa samun ma’aikatar zai magance dukkanin sarƙaƙiyar da ta shafi kiwo, kamar kasuwanci, sufuri da tsaro, maimakon mai da hankali kawai kan kiwo.