Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci a ƙara adadin kasafin kuɗin shekarar 2025 daga Naira tiriliyan 49.7 zuwa Naira tiriliyan 54.2.
Wannan buƙata na ckkin wata wasiƙa da ya aike wa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, wadda aka karanta a zaman majalisar na ranar Laraba.
- Tinubu zai tafi Faransa daga nan ya zarce Habasha
- NAHCON ta tsawaita wa’adin biyan kuɗin Hajjin bana
A baya, Tinubu ya gabatar wa Majalisar Dokoki kasafin Naira tiriliyan 49.7 a ranar 18 ga watan Disamba. 2024.
Sai dai a cikin wasiƙarsa, ya bayyana cewa ƙarin da aka yi ya samo asali ne daga ƙarin kuɗaɗen shiga da hukumomin gwamnati suka tara.
Wannna ya haɗa da Naira tiriliyan 1.4 da Hukumar Tara Haraji ta Ƙasa (FIRS) ta samu, da Naira tiriliyan 1.2 da Hukumar Kwastam ta samu, da Naira tiriliya. 1.8 da wasu hukumomin gwamnati suka samu.
Bayan karanta wasiƙar, Shugaban Majalisar Dattawa, ya tura buƙatar ga Kwamitin Kasafin Kuɗi don yin nazari cikin gaggawa.
Haka kuma, ya tabbatar da cewa za a kammala duba kasafin kuɗin tare da amincewa da shi kafin ƙarshen watan Fabrairu.