✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ne ya lashe zaben Shugaban Kasa —Kotun Koli

Kotun Koli ta tabbatar da hukuncin kotun baya da ta yi watsi da karar Atiku da Peter Obi na zargin murdiyar zaben shugaban kasa na…

Kotun Koli ta tabbatar da Shugaba Bula Ahmed Tinubu a matsayin halastaccen wanda ya lashe zaben Shugaban Kasa 2023.

Mai Shari’a John Okoro ya sanar da cewa alkalan kotun sun yi ittifaki wajen tabbatar da hukuncin da Kotun Saruaron  Kararraikin Zabe ta yanke na tabbatar da nasarar Tinubu a zaben na ranar 25 ga watan Fabrairu.

Kotun ta kuma bayyana cewa samun kaso 25 na kuri’un da aka kada a Babban Birnin Tarayya ba sharadi ba ne na lashe zaben shugaban kasa a Njeriya.

“Atiku da Obi sun gaza kawo alkaluman zaben da suka ci karo da wanda INEC ta gabatar. Saboda haka, sakamakon da INEC ta gabatar shi ne sahihi kuma Bola Ahmed Tinubu ya lashe zaben shugaban kasar Najeriya,” kamar yadda ya sanar.

Kotun ta kuma yi fatali da karar da Atiku, ya shigar da INEC kan matsalar da shafin tattara sakamakon zaben (iREV) ya samu a lokacin zazben na ranar 25 ga watan Fabrairu. Ya kuma bayyana cewa matsalar da shafin ya samu, ba hujja ba ce da za ta sa a soke zabe.

A cikin hukuncin da kotun ta karanta cikin minti biyar ta yi watsi da daukaka karar da tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da kuma Peter Obi na LP suka yi zuwa gabanta.

Alkalan sun kuma yi watsi da karar da aka shigar na takara biyu a lokaci guda da ake wa mataimakin Tinubu, Kashim Shettima.

Kotun ta kuma bayyana cewa babu wata hujja da ke nuna Tinubu ya yi amfani da takardun shaidar karatu na bogi.

Tsohon mataimakin Shugaban Kasa kuam dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, na zargin Tinubu da amfani da takardun shaidar karatu na bogi, don haka yake bukatar a soke nasarar Tinubu.

A bisa haka ne Atiku ya samo kwafi takardar shaidar karatun Tinubu daga Jami’ar Jihar Chicago (CSU) wadda Tinubu ya halarta, da cewa takardun suna da bambaci da wanda Tinubu ya gabatar wa INEC domin tsayawa takara.

A yayin zaman kotun kolin na ranar Alhamis, kwamitin alkalai bakwai na kotun ya yi watsi bukatar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar na gabatar mata da sabbin hujjoji kan zargin.

Alkalan sun kara da cewa, hasali ma babu wata hujja da ke tabbatar da Shugaba Tinubu da amfani da takardun bogi.