✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ne ya haddasa zanga-zanga —Gwamnan Bauchi

Gwamnan Bauchi ya caccaki Tinubu kan jawo wahalhalu da tsadar rayuwa a Najeriya

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya sake caccakar shugaban kasa Bola Tinubu kan manufofinsa na tattalin arziki da ya ce sun kara jawo wa ‘yan Najeriya talauci yunwa da fushi da kuma da tsadar rayuwa, shi ya sa ake zanga-zangar kawo karshen mulkin wahala a kasar.

Gwamnan ya soki jawabin da shugaban kasar ya yi a ranar Lahadi da ta wuce ga al’ummar Nijeriya, inda ya ya ce jawabinsa holoko ne babu komi a ciki, kuma ya gaza magance korafe-korafen matasan da suka yi zanga-zangar adawa da yunwa da kuncin rayuwa.

A cewarsa, shugaban kasar bai tuntubi gwamnoni ba, wadanda su ne mutane na farko da ya kamata ya fara karbar bayani daga wurinsu, saboda su ne suke kusa da ’al’ummar kasa.

Gwamna Bala ya bayyana haka ne a lokacin da yake kaddamar da yakin neman zaben jam’iyyar PDP gabanin zaben kananan hukumomin jihar da za a yi ranar 17 ga watan Agusta.

Ya ce, “matasan da suke zanga-zangar suna tare da mu kuma muna tare da su. Mu a koyaushe muna mutunta mutane, musamman ra’ayinsu.

“Zanga-zangar ta nuna mana abubuwa da dama. Ga dukkan alamu Jam’iyyar APC ba ta yi komai ba.

“Na saurari jawabin da shugaban kasa ya yi gaba daya, na ce, cikin tawali’u da jajircewa, abin da ya fada ba komai ba ne!

“Bai yarda da lamarin ba. Bai magance matsala da balubale ba. Matsalolin ba matasa kadai ba ne, namu ne a matsayinmu na shugabanni – tun daga kan shugaban kasa har zuwa gwamnoni da kananan hukumomi, kuma muna iya ganin abubuwan da suka faru da launuka daban-daban – daga Arewa zuwa Kudu.

“A Arewa akwai babban kira na farkawa, da zai kawo mana shugabanci nagari, mu mutunta mutane.

“Akwai yunwa da fushi. Dole ne mu magance matsalarmu ta ci gaba; Rashin aikin yi yana ko’ina, tsarin ilimin mu ba ya aiki.

“Sabbin manufofin gwamnatin tarayya ba sa aiki, dole ne su fahimci hakan. Matsalarsu ce. Shirye-shiryensu ne suka jawo mana wadannan matsaloli, don haka dole su canza.”

Gwamnan ya ce gwamnatin jihar a shirye ta ke ta sauya salon yadda za ta samar da shugabanci na gari “ba wai ta yi tunanin lokaci ya yi da za ta wuce gona da iri ba, ta zargi gwamnoni ko kananan hukumomi.

“Na ji, wasu ministocin da ke cewa an ba mu manyan motoci 70, N570bn, nawa ne gwamnatin tarayya ta samu?

“Me ya sa za su kawo manufofin da ke haifar da ciwo? A madadinku, ina gaya wa shugaban kasa, Tinubu, ya canza manufofinsa domin ba ta aiki.

“Duk abin da yake yi ya shafe mu a kowane lungu, a kowace jam’iyya, a matsayinmu na shugabanni.

“Idan ya ci gaba a haka, a 2027, zai zamo yana mana yakin neman zabenmu ne – domin ko’ina za ta zama PDP kuma za mu yi nasara.”

Gwamnan wanda shi ne Shugaban kungiyar gwamnonin PDP ya ce takwarorinsa na PDP sun saurari masu zanga-zangar ciki har da gwamnonin APC amma gwamnatin tarayya ta kan ba da uzuri.

Ya ce, “waya kawo Yunwa? Waya kawo zanga-zanga? Wa ya kawo mana tsadar rayuwa?Wa ya kawo yunwa da fatara?” magoya bayansa na kuwwa suna cewa Tinubu.