Jagoran jam’iyyar APC na kasa kuma tsohon Gwamnan Jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu, na taro da Gwamnonin jam’iyyar a ranar Litinin.
Taron, wanda ke gudana a masaukin Gwamnan Jihar Kebbi da ke unguwar Asokoro a Abuja, na zuwa ne ’yan sa’o’i bayan Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya ayyana tsayawa takara a zabe mai zuwa.
- Buhari ya tsawaita lokacin ritayar malaman makarantu da shekara
- Gwamnati na son cire ’yan Najeriya miliyan 40 daga talauci cikin shekara 2
Daga cikin Gwamnonin da suke halartar taron har da na Kebbi (Atiku Bagudu) da na Jigawa (Badaru Abubakar) na Osun (Gboyega Oyetola) da na Legas (Babajide Sanwo-Olu) da na Filato (Simon Lalong) da na Kaduna (Nasiru El-rufa’i).
Da sanyin safiyar Litinin ce dai Farfesa Osinbajo ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar a karkashin jam’iyyar APC a zabe mai zuwa.
Tun gabanin ayyana takarar tasa ma, Osinbajon shi ma ya karbi bakuncin wasu Gwamnonin APC domin buda-baki ranar Lahadi.