✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu na cikin koshin lafiya —Inji hadiminsa

Hadimin ya ce jagoran ba shi da wata cuta da take bukatar kwanciya a asibiti.

Hadimin Jagoran Jam’iyyar APC Asiwaju Bola Tinubu, Tunde Rahman ya karyata labaran da ake yadawa cewar mai gidan naa na kwance a asibiti.

Tunde Rahman ya ce Tinubu na cikin koshin lafiya, sabanin rade-radin da ake cewar tsohon gwamnan Jihar Legas din na kwance a wani asibiti da ke Maryland a kasar Amurka.

  1. Yadda uwa ta kashe ’yarta kan yawon ta-Zubar
  2. ’Yan bindiga na bore kan sauke sarki a Zamfara

Ya ce, “Mai girma Asiwaju Bola Tinubu yana nan lafiya. Yana cikin koshin lafiya. Ba shi da wata cuta da take bukatar kwanciya a asibiti. Tabbas, yanzu ba ya nan ya yi tafiya zuwa kasar waje amma zai dawo ba da jimawa ba.

“Duk lokacin da ya yi tafiya zuwa kasar waje surutan ta ke biyo baya su ne cewa ba shi da lafiya ko an kwantar da shi a asibiti ko kuma ya mutu; Wannan abun kunya ne ga masu yada irin wadannan karerayin kuma asirinsu na tonuwa ta yadda ake gane labaran karya suke yadawa.

“Wane ne ke tsoron Asiwaju Tinubu? Duk masu masa fatan sharri ko mutuwa su bi a hankali. Ya kamata su san cewa rayuwa da mutuwa na hannun Ubangiji,” a cewarsa.

Tun bayan ficewar jagoran daga Najeriya rahotanni ke ta yawo cewa an fitar da shi kasar waje ne don nema masa lafiya.