✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu bai ba kowa damar tattaunawa da ’yan ta’adda ba – Abdulaziz

Sai dai hadimin ya ce a yanzu babu wanda gwamnatin ta bai wa damar yin sulhu da 'yan bindiga.

Abdulaziz Abdulaziz, hadimin Shugaban Kasa Bola Tinubu kan kafofin watsa labarai, ya ce gwamnatinsu ba ta wakilta kowa ba domin ya tattauna da ’yan ta’adda ba.

A wata hira da ya yi da DCL Hausa, Abdulaziz ya ce gwamnati a shirye ta ke ta yi amfani da duk wata hanya don samar da zaman lafiya a kasar.

Ya ce, “Gwamnatin Tarayya, Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, da sauran jami’an gwamnati ba su bai wa kowa izini ya tattauna da ’yan ta’adda ko ’yan fashi a hukumance ba.

“Gwamnatin tarayya ba ta da hannu a duk wata tattaunawa da ’yan bindiga. Wannan ba maganar gwamnati ba ce, amma kamar yadda shugaba Tinubu ya ce a farkon gwamnatinsa, gwamnati a shirye ta ke ta yi amfani da kowace hanya don kawo karshen ’yan fashi, asarar rayuka da dukiyoyi, da tashe-tashen hankula a sassan kasar nan.

“Abu na biyu kuma shi ne, dole ne mu amince da cewa akwai wurare da dama a Najeriya da sauran kasashen duniya da aka dauki lokaci mai tsawo ana fama da rikici wajen magance amfani da makamai.

“Akwai wata magana da ke cewa ‘kowane rikici yana karewa ne a kan teburi.’ Shi ya sa wasu ke kallon sakamakon tattaunawa da tsagerun Neja-Delta da wasu a baya a kasar nan, shi ya sa wasu ke ganin ko irin wannan hanya za ta iya aiki a arewa.

“Duk da cewa gwamnati ba ta fara wannan tattaunawar ba, amma kofa a bude ta ke idan aka gano cewa ita ce hanya mafi kyawun wanzar da zaman lafiya.

“Manufar ita ce a samar da zaman lafiya a daina kashe talakawa. Don cimma wannan, gwamnati a shirye ta ke ta yi amfani da duk hanyoyin da ta samu.

“Mun kuma samu labarin cewa wasu shugabannin al’umma da masu ruwa da tsaki na kokarin ganin an shawo kan matsalar ba tare da amfani da makamai ba. Idan irin wadannan hanyoyin sun samun, bai kamata a kashe musu kwarin gwiwarsu ba.

“Gwamnatin Bola Ahmad Tinubu na fatan ganin ta kawo karshen wannan matsala, ta hanyar amfani da makamai ko akasin haka. Za mu yi duk abin da za mu iya, da yardar Allah, don kawo karshen wannan ta’addanci da aka shafe sama da shekara 10 ana yi,” a cewar Abdulaziz.