✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinkahon taratsin tattaunawar tarho

Tartsatsin taratsin tinkaho Tantagaryar tattaunawar tarho Taho-taho Tumfafiya tai toho Tawayar tangaraho   Batun buhun bankare baho Gingimemen garmaho Balli-ballin tsinin kaho Tsuwwar dan tsakon…

Tartsatsin taratsin tinkaho

Tantagaryar tattaunawar tarho

Taho-taho

Tumfafiya tai toho

Tawayar tangaraho

 

Batun buhun bankare baho

Gingimemen garmaho

Balli-ballin tsinin kaho

Tsuwwar dan tsakon bakin shaho

Takun tattakin taho-taho

 

’Yar gatan Iya-talle

Maman-tine ta sake lale

Lanhonta kamar an kyale

Batun ga ko an daddale

A ce nai tsurku a gidan Baballe

 

Kurtun maganar walle-walle

Kade-kade da tsalle-tsalle

Sai an buga kidan talle

’Yan wasa an yi adon kyale-kyale

Zillaziyya na zille-zille

 

’Yan sisi

Hukuma tai kwafsi

Ana ta kwasar asi

Layin waya mai jefa wasi-wasi

Dole ne a bi ba’asi

 

Garmar tunkude talauci

Asusun masu fatauci

Lalitar masu dukanci

Tara matsabbai akwai azanci

Baba dai ya hana cin hanci

 

Wasu na ta dabbanci

A daina yi wa juna batanci

Sara-sukar iskanci

Sha’anin shawaraki shashanci

Keta doka na sa a shiga kunci

 

An cefanar mini layi

An sanya ni laulayi

Salalar salular layi

Ina ta samun wayoyi

Lallai labin ga na da kayoyi

 

Gaye mai hululu

Ya bijiro min da batun Kulu

Ko yana nufin mai sakar ulu

Ina Jamila da Jamilu

Mu je gaban Malam Sahlu

 

Ana ta dumbuzo mini matsabbai

Adadinsu ya dara kwabbai

Kar fa a nunke ni a baibai

Na san Dabai

Ba na karyar sanin Dubai

 

Wata ta yasar da waya

Kawaye na ta bibiya

’Yan lalle na ta tambaya

Lambar kulu ce tai zirya

Mai tagwayen suna ta shige kurya

 

Nanu nunin Fadima

’Yar makaranta mai himma

Ki kara kwazo da azama

Ki zanki sanin makama

Kwarewarki za ta taimaki al’umma

 

Bobo karamar Dodanniya

Fici da Nanawo ’yan uwa

Neman ilimi ba a kuwwa

Sai fafutikar kokowa

Yaki jahilci a Haurobiya

 

Malam Na-kwaciri

Ja na-zomon adon gari

Su daina tsirfa iri-iri

Kar su afka garari

Batun ingarma a fito sarari

 

Cikin watan Noman-Baba na shekarar da ta rare a guje, wato dubu karamin lauje da silin madambaci, kurtuna na halo alalo ya samu tangarda, don haka sai na sake sayen wasu layuka, na Iya-talle da Maman-tine na makala a sabon kurtun yin batu, amma abin mamaki har cikin shekarar nan ta dubu karamin lauje da sili da manuniyar kasa ba a daina laluben wadannan layuka nawa da zimmar neman adon-gari, Mai tagwayen suna; wata rana kuwa aka bijiro mini da bukatar layin salular Kululu, amma fa ba Mai-tuwo uwargidan Lado ba.

Wadannan lamura da ake ta tsuwurwurta mini a cikin kurtun maganata sun sa na yi ta hankoron cafke ’yan wala-wala, masu walle-walle, suna ta tsalle-tsalle, kamar ana yi musu kidan talle. Idan kuwa ba su ba ne, ai sai a ce ko tangardar tangaraho ce, ko kuma gangin gingimemen garmaho ne. Haurobiyawa hakika Adon-gari da ’Yan lalle ne ke yi mini tumbalale-tumbalale. Ta yiwu kuma masu laluben Santaleliyar Santala ce ko Santalele Salele.

Tartsatsin taratsin tinkahon tattaunawar tarho ai sai iyayen al’umma, musamman a zamanin da koshiyar Na-talle ke sharafinta, kafin Baba-ojo da kanensa su cefanar da ita; kodayake yanzu ma Adon-gari da ’Yan lalle na baza batutuwa a cikin kurtun halo alalo, har da tsirfa iri-iri. Wadannan batutuwa buhu-buhun bankare baho da suka cika mini tumbi sai na sanar da Malam Na-kwaciri, shi kuwa tuni ya yi nazari, inda ya fasko cewa wasu ne suka afka cikin garari, don haka suke ta laluben abokin balaguro.

Wani abin ban ta’ajibin ma, shi ne har GARMAR TUNKUDE TALAUCI ta tunkudo mini sakon Allah Ya raya, don murnar zagayowar ranar haihuwar Mai tagwayen suna ’yar Haruna, amma dai har yanzu ba su jinko mini damin matsabbai; ko sakon ankararwar shige da ficen matsabbai a asusun Mai tagwayen suna ba.

’Yan makaranta kai har damin matsabban yin batu aka yi ta antayo mini a wadannan layuka salula. Abin da na guda dai irin wancan Man-kazar na bayan kangon Amintacciyar jaridar kasar Haurobiya ne ya samu wannan gwaggwabar garabarasa, ai sai cin gurasa, ko ma ya kan ga gilashi ya yi ta yaren Ingilishi kamar yana cin kilishi. Idan kuwa DAN GIDAN Mai motar Roba ne ya samu wadannan layukan burga da baragada zai rika yi wa adon-gari, irin na ’yan bokoko; BOBO DA KWAMBO SAI DAN BOKO. Watakila ma ya rika yi musu burga da cewa ya san suna motar kawunsa kamar yadda aka taba bayyanawa a farfajiyar wannan makaranta, wato ROBORIOUS MOTORIOUS – RUBBER ROBOTIC MOTORISED CAR.

Batu dai na ingarman karfen karafan layin tarragon titin dogo, ba tare da bata lokacin wulwulawar agogo ba, Malam Na-kwaciri ya yi nuni da cewa ’YAN SISI ce ta yi kwafsi, inda ta bari Maman-tine ta cefanar da layin MAI TAGWAYEN SUNA, bayan da ta yasar da shi na tsawon lokaci. Shi ma na Iya-tallen, tunda hawainiyar kurtun magana ce ko tantama babu na wani ne ko wata aka cefanar mini bayan da aka dauki tsawon lokaci ba a ji BAMBAMIN BATUTUWA BA!

Baban-burin-huriyya a umarci Iro mugun madambaci ya durfafi masu damfararar damun fura a kurtuna magana, tun kafin su damalmala al’amura, musamman daidai wannan lokaci da Haurobiyawa ke tunkarar ZABABBAKAR ZABUKAN shekarar dubu karamin lauje da silin manuniyar kasa. Kada mu yi kasa a gwiwa wajen nusar da hukuma masu tsiwurwurta ta’asa a kwanon tasarsu!