✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Tilasta wa Tanko Muhammad aka yi ya sauka daga mukamin Alkalin Alkalai’

Majiyoyi sun ce Fadar Shugaban Kasa ce ta tilasta masa sauka

Wasu majiyoyi masu yawa sun tabbatar wa Aminiya cewa ajiye mukamin da Alkalin Alkalan Najeriya, Ibrahim Tanko Muhammad ya yi an jima ana tsara shi kuma tilasta masa aka yi ya sauka.

Jim kadan da ajiye aikin Ibrahim Tanko dai, Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Litinin ya rantsar da Mai Shari’a Olukayode Ariwoola, wanda shi ne na biyu a Kotun Koli, a matsayin sabon Alkalin Alkalan na Najeriya.

Yadda aka tilasta wa Tanko ya sauka

Alamomi sun fara bayyana cewa akwai matsala ranar Litinin bayan da aka gaza ganin fuskar Mai Shari’a Tanko a wajen bikin bude taron horar da alkalan Majalisar Alkalai ta Kasa (NJC) kan hanyoyin warware rikice-rikice a Abuja.

Tanko dai bai halarci taron ba ba tare da ya fadi dalili ko ya tura wakili ba.

Hatta hadimansa sun ce ba su da masaniya kan shirin nasa na ajiye aiki sai da afiyar ranar ta Litinin.

Sai dai wasu majiyoyi sun tabbatar wa Aminiya cewa an umarce shi da ya bayyana a Fadar Shugaban Kasa, inda aka damka masa takardar ajiye aikin aka kuma umarce shi da ya rattaba hannu a kanta.

Kazalika, Aminiya ta gano cewa an jima ana kulle-kullen ganin hakan ta tabbata, kuma wani babban jami’in gwamnati kuma jigo a bangaren tsaro ne ya jagoranci batun.

An kuma hada da manyan jami’ain NJC a cikin shirin.

Wata majiya ta tabbatar mana cewa tun bara aka tsara ganin ya ajiye mukamin nasa, amma aka jira sai da Mai Shari’a Mary Odili ta ajiye mukaminta, wacce da ta hau kujerar kasa da shekara daya kawai za ta shafe a kai.

An dai bayar da batun rashin lafiyar Tankon ne a matsayin dalilin ajiye mukamin nasa.

Wani babban lauya mai mukamin SAN, wanda ya yi magana bisa sharadi a sakaya sunansa, ya ce tsohon Alkalin Alkalan tilasta masa aka yi ya sauka daga mukamin nasa saboda dalilai guda biyu – wasikar da alkalai suka rubuta masa da kuma wasu badakalolin kudade.

Ya ce an yi amfani da rashin lafiyarsa ne a matsayin dalili, wanda dukkan masu ruwa da tsaki a harkar shari’a suna sane da shi, amma aka kyale shi har zuwa karshen Disambar 2023, lokacin da ya kamata ya yi ritaya.

‘Tun cikin dare aka karkare shawarar cire shi’

Kazalika, wata majiyar da ita ma ta nemi a sakaya sunanta ta ce tsohon Alkalin Alkalan tun dare Lahadi aka fitar da shi daga cikin gidansa zuwa wani wajen da babu wanda ya sani.

“Da zuwa wajen gidan sai suka damka masa takardar ajiye aikin suka kuma bukaci ya rattaba hannu a kai. Sun shaida masa daga Shugaban Kasa aka aiko su, a kan haka dole ya sanya hannun. Ko shawara ba a bar shi ya yi ba, ko da da iyalansa,” inji majiyar.

Sai dai wata majiyar daga Kotun Koli ta ce tsohon Alkalin Alkalan ya sha fama da rashin lafiya, wacce ta rika shafar yadda yake gudanar da aikace-aikacensa.

“A cikin watan Azumin Ramada, Shugaban Kasa ya gayyaci alkalai bude-baki, amma Tanko ya tsara tafiya Kaduna a lokacin, da aka tina masa, sai ya ce bai san da gayyatar ba, duk kuwa da cewa an fada masa tun da wuri,” inji majiyar.

A ranar 21 ga watan Yunin nan ne dai Alkalan Kotun Koli suka rubuta wasika suna zarginsa da rub-da-ciki a kan wasu kudade, wacce dole ya mayar da martani daga bisani.