✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tilasta koyar da harshen Faransanci

Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin cewa daga yanzu dalibai a kowane matakin karatu a kasar nan daga firamare zuwa jami’a, wajibi ne su a…

Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin cewa daga yanzu dalibai a kowane matakin karatu a kasar nan daga firamare zuwa jami’a, wajibi ne su a koyar da su harshen Farasanci.  Minista a Ma’aikatar Ilimi Farfesa Anthony Anwukah ne ya bayyana haka kwanan nan lokacin da Jakadan Faransa a Najeriya Denys Gaber ya kai masa ziyarar girmamawa a Abuja.
Minista Anwukah ya ce, “Koyon Harshen Faranci ya zama lalura. Saboda kasashen Kamaru da Nijar da Chadi da Jamhuriyar Benin da Togo da Guinea da Kwaddibuwa sun kewaye mu, don haka akwai bukatar mu samun karin ’yan Najeriya da za su kware a harshen Faransanci.” Kuma a yayin da yake bayani kan samar da karin malamai masu koyar da harshen Faransanci, ministan ya ce kwanan nan gwamnati za ta fara da karin horo ga malaman harshen Faransancin. Ministan ya kuma kaddamar da Cibiyar Koyar da Faransanci a Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Maza da ke Apo, Abuja.
Anwukah ya ce Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya tana da burin kafa cibiyoyin koyar da Faransaci a dukkan kwalejojin Gwamnatin Tarayya da ke kasar nan. Cibiyoyin ana sa ran su inganta ginshikai hudu na koyo ga dalibai da suka hada saurare da furtawa da karantawa da kuma rubutawa.
Wannan matsayi na Gwamnatin Tarayya na tilasta nazarin harshen Faransanci a makarantu da manyan cibiyoyin ilimi wani babban abin yabo ne. yana da kyau ga kasar nan musamman mutanen da ke garuruwa da kauyukan kan iyakokin. Idan suka iya harshen Faransanci hakan zai taimaka musu wajen inganta huldar tattalin arziki da rayuwa a tsakanin ’yan Najeriya da makwabtansu masu magana da harshen Faransanci. Karanta harshen Faransancin zai kuma sanya daliban Najeriya su dada gasa a matakai daban-daban na duniya.
Sai dai ba wannan romon baka ba ne, akwai bukatar gwamnati ta bi bayan magana da aiki ta bullo da tsare-tsaren da suka wajaba a fili balo-balo a cikin Tsarin Ilimi na kasa, musamman abin da ya shafi babbar sakandare da manyan cibiyoyin ilimi. Akwai wannan tsari a kananan makarantu. A manyan cibiyoyin ilimi za a iya sanya shi a cikin rukunin manyan darussan da ake nazari da za a bukaci dalibai su cinye su kafin su samu gurbin zuwa manyan makarantu a Najeriya. Wannan dabara a sabuwar yanayinta za ta dada kara sha’awar dalibai ga karanta harshen Faransanci na dogon lokaci,
A duniya wadda take dada komawa karama, yana da muhimmanci ’yan Najeriya su fahinmta tare da girmama mabambanta al’adu na mutanen kasashen waje. Nazarin harshen Faransancin zai ba ’yan Najeriya damar sani da fahimtar al’adun dukkan kasashen da suke magana da harshen Faransanci. Kuma zai kara musu dama ta samun aiki a hukumomin kasashen da ke amfani da harshen Faransanci a ciki da wajen kasar nan.
Idan za a iya tunawa gwamnatin marigayi Janar Sani Abacha ta sanya koyon harshen Farasanci wajibi a makarantun firamare da kananan sakandare na Najeriya. Wannan ya shafi shekara tara na shirin bayar da ilimi kyauta a matakin farko na ilimin. Manhajar Ilimi ta shekara tara da ake amfani da ita yanzu, ta wajabta karantar harshen Faransanci a matakai na tsakiya da na sama na ilimi a matakin farko, wanda yake faraway daga aji hudu na firamare zuwa shekarar karshe ta karamar makarantar sakandare.
Baya ga haka, akwai bukatar mu samu kayayyakin da suka wajaba wajen koyar da harshen Faransancin a makarantun, kuma nasarar wannan darasi mai muhimmancin galibi ya dogara ne kan samar da wadatattu kuma kwararrun malaman koyar da Faransancin. Don haka gwamnatin kasar Faransa za ta iya kyautatawa ta hanyar bayar da tallafi a bangarorin malamai da kayayyakin koyarwa. Domin haka mun goyi bayan kiran da Minista a Ma’aikatar Ilimin ya yi lokacin da ya bukaci Jakadan Faransa a Najeriya kan ya duba karin hanyoyin tallafa wa gwamnatin Najeriya cikin gaggawa wajen horar da malaman harshen Faransanci na matakan makarantun firamare da sakandare da manyan cibiyoyin ilimi.
Wajibi ne gwamnati ta aiwatar da Shirin Cibiyar Koyar da Faransanci kamar yadda ta tsara, kuma ta kauce wa duk wani dalili ko matsala da za su jawo a yi watsi da shi. Hukumomin makarantu da malamai a karfafa musu kan yadda za su jagoranta tare da sanya ido kan dalibai su yi amfani da cikakkiyar wannan dama ta cibiyar koyar da Faransanci ta hanyar koya da cin amfani wannan shiri.