Fasinjojin a tashar jiragen kasa ta Rigasa da ke Kaduna sun koka kan yadda suka ce ’yan ka-yi-na-yi sun sare tikitin tare da tsauwala musu kudi.
A sakamakon haka, tilas fasinjoji suka rika sayen tikitin a kan farashi mai dan karen tsada a hannun ’yan sari.
- ‘’Yan bindiga suna aikata ta’addanci amma ba ’yan ta’adda ba ne’
- Mun bankado sunan jariran da ake biya albashi daga lalitar Borno – Zulum
Aminiya ta gano cewa tun kusan ranar Juma’a ne dai shafin sayar da tikitin ta intanet na Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC) ya daina aiki, lamarin da ya sa fasinjoji suka koma saye a tashar.
Hakan dai ya sa wasu ma’aikatan hukumar hada baki da ’yan ka-yi-na-yin, wadanda suka sare tikitin.
Lokacin da wakilinmu ya ziyarci tashar da misalin karfe 7:00 na safe, ya iske cincirindon fasinjoji da suka gaza sayen tikitin a jirgin karfe 6:40 sun bi layi don saye a na karfe 10:30.
To sai dai daga bisani ’yan sari sun rika shiga layi inda suka rika sayen tikiti uku zuwa hudu, sannan suna sayarwa a farashi mai tsada.
Aminiya ta gano cewa ana sayar da kowanne tikiti tsakanin Naira dubu uku, dubu biyar zuwa dubu bakwai ga fasinjoji da ke kokarin kauce wa masu garkuwa da mutane hanyar zuwa Abuja ta mota.
Wani mazaunin Kaduna, wanda ya je tashar wajen misalin karfe 8:30 na safe, ya ce lokacin da ya je wurin, an shaida masa cewa babu tikitin jirgin karfe 10:30, inda aka ba shi shawarar ya jira wani jirgin.
Sai dai ya ce dole ta sa ya hakura ya sayi tikitin a hannun ’yan sari kan N7,000.
Har zuwa misalin karfe 10:13 da jirgin ke shirin tashi dai, fasinjoji na ta zama a kan layi don sayen tikitin.