Asusun Tallafa wa Manyan Makarantu na Najeriya (TETFund) ya fara amfani da Kungiyar Dalibai ta Najeriya (NANS) wajen duba gine-ginen da yake yi a makarantunsu.
Shugaban asusun, Sunny Echono ne ya bayyana hakan lokacin da yake bayar da kyautar wata motar bas mai cin mutum 30 ga NANS a Abuja ranar Litinin.
Ya ce daukar matakin ya zama wajibi saboda a rika sanya idanu yadda ya kamata a kan ’yan kwangilar da ke yin ayyukan.
Sonny ya kuma ce idan suna amfani da daliban, hakan zai sa su kasance suna da idanu da kunnuwa a makarantun, musamman kasancewar su daliban ne za su amfana da ayyukan.
Shugaban na TETFund ya kuma ce sun ba kungiyar gudunmawar motar ce domin saukaka musu zirga-zirga a tsakanin makarantu.
Da yake mayar da jawabi, shugaban NANS, Usman Barambu, ya yaba wa asusun saboda kyautar motar, bayan rokon da suka yi ga Shugaban Kasa Bola Tinubu a kwanakin baya.