✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ɗalibai za su rufe manyan biranen Najeriya kan ƙara farashin fetur

Ɗaliban sun ce ba za su zuba ido wasu tsiraru su kassara makomarsu ba.

Ƙungiyar Ɗalibai ta Ƙasa (NANS), ta sanar da shirin rufe dukkanin manyan biranen Najeriya daga ranar 15 ga Satumba, kan ƙara farashin man fetur.

NANS ta bayyana cewar za ta gudanar zanga-zangar ne a matsayin martani kM ƙarin farashin man fetur da aka yi a farkon makon nan.

A ranar Talata ne, aka samu ƙarin farashin man fetur daga Naira ₦568 zuwa ₦855 kan kowace, kuma an aiwatar da hakan ne a duk gidajen mai na Kamfanin NNPC.

Ƙarin farashin ya haifar da cece-kuce a faɗin ƙasar, inda ƙungiyoyin ma’aikata suka nemi a sauya sabon farashin nan take.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, shugaban Ƙungiyar Ɗalibai ta Ƙasa (NANS), Okunomo Henry Adewumi, ya buƙaci a gaggauta janye sabon farashin man fetur.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, za a gudanar da zanga-zangar ne cikin lumana kamar yadda doka ta tanada.

“Mun rubuta ne domin sanar da ku game da wani gagarumin rufe dukkanim manyan biranen Najeriya, daga ranar 15 ga Satumba, 2024, domin nuna adawa da ƙarin farashin man fetur da aka yi.

“Ƙarin farashin da aka samu, ya jawo wa talakawa wahala, kuma ba za mu zura ido yayin da makomarmu ta dogara ga wasu tsiraru.

“Muna kira ga ɗaukacin ɗaliban Najeriya da su farka da wannan kira na faɗakarwa, domin za mu mamaye manyan biranen ƙasar nan a ranar 15 ga Satumba, 2024.

“Ba za mu yi shiru ba, kuma ba za a tsorata mu ba. Za mu tashi tare domin neman ingantacciyar yarjejeniya ga ɗaliban Najeriya da talakawa.

“Muna roƙonku da ku ɗauki matakan da suka dace don tabbatar da doka da oda yayin rufe biranen, yayin da muke ba ku tabbacin cewa zanga-zangar tamu za ta kasance cikin lumana da doka,” in ji sanarwar.