✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Tell Your Papa’: NBC ta haramta amfani da waƙar da ke sukar Tinubu

NBC ta shaida wa kafofin labaran Nijeriya cewa waƙar ta saɓa ƙa’ida da ma taɓa “mutuncin gwamnati.”

Gwamnatin Tarayya ta haramta amfani da wata sabuwar waƙar da ke sukar Shugaba Bola Tinubu a dukkanin kafofin labarai na rediyo da talabijin a faɗin ƙasar.

Waƙar da mawaƙi Eedris Abdulkareem ya fitar a baya-bayan nan mai suna“ Tell Your Papa”, ta soki yadda Shugaba Tinubu ke gudanar da tattalin arzikin Nijeriyar.

The lyrics are addressed to Tinubu’s son, calling on him to let his father know “people are dying” from economic hardship as well as continued insecurity from armed groups.

Baitocin waƙar da ke ɗauke da kira ga ɗan shugaban ƙasar, Seyi Tinubu, sun buƙaci ya isar wa mahaifinsa saƙon cewa ’yan Nijeriya na fama da matsanancin ƙunci na tattalin arziki da kuma matsalar tsaro.

Sai dai Hukumar Kula da Kafafen Watsa Labarai a Najeriya NBC, ta shaida wa kafofin labaran ƙasar cewa waƙar ta saɓa ƙa’ida da ma taɓa “mutuncin gwamnati.”

Tuni dai mawaƙi, Eedris Abdulkarim, ya mayar da martani, inda ya buƙaci magoya bayansa su saurari waƙar ta hanyoyin da kafar Intanet ta bayar da dama.

Abdulkareem ya wallafa a shafinsa na zumunta cewa, faɗa wa gwamnati gaskiya ko sukar gyara kayanka a kullum laifi ne a Nijeriya.

Shekaru biyu na mulkin Bola Tinubu a ƙasar dai sun gamu da zanga-zanga musamman kan tsadar rayuwa da man fetur.