Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya (ABU) ta bayyana cewa binciken fasaha ne ya samar da sabon irin masara da ake wa lakabi da Tela Maize wanda babu wata nau’in cutarwa a tattare da ita.
Farfesa Rabiu S. Adamu na Cibiyar Binciken Aikin Gona (IAR) da ke Jami’ar ABU ne ya jagoranci tawagar masu bincike wajen samar da sabon irin na Tela Maize domin amfanin manoman Najeriya.
Ya ce jita-jitar da ake yadawa cewa sabon irin yana da illa ga lafiyar mutane babu kamshin gaskiya, kuma akwai nau’in hasada a farfagandar.
Ya ce duk haka masu yada jita-jitar a kafofin yadda labarai na zamani sun kasa bayyana inda suka gudanar da nasu binciken da har suka gano cewar Tela Maize tana da illa ga lafiyar dan Adam.
Jami’in binciken ya bayar da misalin lokacin da aka shigo da takin zamani, inda manoma suka kyamace shi, duk da cewa kyauta ake ba su.
Haka nan, ita kanta masara a lokacin da aka fara kawo ta manoma sun kyamace ta, amma yanzu da aka fahimci amfaninsu sai neman su ake yi.
Farfesa Rabiu ya shawarci manoma da su yi watsi da muguwar shawarar marasa son cigaba da bunkasar aikin gona a kasa.
Ya ci gaba da cewa Tela Maize ba ta bukatar maganin feshi da sauran dangoginsu.
Sannana tsutsar da ke lalata masara a gona ba ta iya yi wa Tela Maize komai, ga ta kuma da jure fari.
Tuni dai Gwamnatin Tarayya ta amince da sabon irin masarar Tela Maize kuma ta bayar da dama a raba wa manoma domin a yada shi a fadin asar nan.