Kwana daya kacal da kara farashin man fetur ’yan kasuwa sun kara farashin kayan abinci na da ababen surufi a Jihar Taraba.
Kafin a kara kudin man fetur ranar Talata an sayar da kwanon shinkafa ’yar gida N3,100, amma farashin ya koma N3,400.
Sai kuma masara da doya da wake wadanda su ma aka kara.
Masu babur mai kafa uku da masu motocin haya su ma sun kara kudin haya a kan hanyoyin garin Jalingo da sauran sassarn jihar.
- Harajin da ake karɓa a Najeriya ya yi kaɗan — Bill Gates
- A gaggauta soke karin kudin fetur —NLC
- Za mu gyara ‘bohol’ 25 a kan N1.2bn —Gwamnan Sakkwato
Masu gidajen man fetur suna sayar da Lita daya na man fetur akan kudi Naira dubu daya da Naira Dari.
Binciken wakilin Aminiya ya nuna cewa masu sayar da man fetur ta bayan fage na sayar da Lita daya na man fetur akan kudi Naira dubu daya da Naira Dari uku.
Wasu mazauna garin Jalingo da aka zanta da su sun nuna rashin jin dadinsu kan karin farashin man fetur da Gwamnatin Tarayya ta yi.
Dauda Adamu, maiakacin gwamnatin Jihar Taraba, ya ce, “da ma kafin farashin man fetur jama’a na fuskantar tsadar rayuwa.
“Karin farashin man fetur da aka yi jiya zai kara wa talakawa matsatsin rayuwa.”
Ya nemi Gwaamnatin Tarayya ta janye wannan karin in dai tana da tausayin al’umma.