Gwamnan Jihar Neja Abubakar Sani Bello, ya gana da iyayen dalibai 136 na makarantar Islamiyyar Tanko Salihu, da ke garin Tegina da ’yan bindiga suka yi awon gaba da su a makonnin da suka gabata.
Ana iya tuna cewa, a yayin da lamarin ya auku, Gwamna Bello ya fita ziyarar aiki a ketare inda ya halarci wani taro da ya shafi matsalolin tsaro da suka addabi jiharsa.
- ’Yan bindigar da suka sace ’yan makarantar Yawuri sun fitar da hotunansu
- Masu zanga-zangar neman Buhari ya sauka sun fara kone-kone a Abuja
A kan haka ne Gwamnan bai samu damar ganawa da iyayen daliban ba sai a wannan lokaci bayan dawowarsa a makon da ya gabata.
A safiyar Litinin ce Gwamnan bayan ganawa da wasu masu ruwa da tsaki a jihar kan rikicin da ya barke tsakanin wasu ’yan banga da wasu matasa, kai tsaye kuma ya wuce garin Tegina inda ya gana da iyayen daliban.
Bayanai sun ce Gwamnan ya gana da iyayen daliban a fadar Sarkin Kagara, Alh. Ahmed Garba Gunna, inda ya jajanta musu dangane da halin da suka shiga, sannan ya ba su tabbacin cewa gwamnatinsa na iya bakin kokarinta don ganin ta ceto daliban cikin koshin lafiya.