Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya dakatar da Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya na jihar, Dakta Isah Adamu.
Sai dai babu wani cikakken bayani game da dalilin da yasa aka dakatar da shi, amma Aminiya ta tattaro cewar hukuncin na da nasaba da rashin jituwar da ta kunno kai kan batun malaman firamare, yayin da wasu majiyoyin suka ce siyasa ce kawai.
- Ni na ankarar da Buhari ’yan bindiga na neman sace shi —El Rufa’i
- Tsaf ’yan ta’adda za su iya sace Buhari —Naja’atu
An umarci Daraktan hukumar na uku, Alhaji Abdulkadir Shehu Nafuntua, ya karbi ragamar tafiyar da harkokinta nan take.
Sai dai tuni wasu malaman makaranta a jihar suka shiga dandalin sada zumunta na Facebook suna nuna farin cikinsu kan matakin da Gwamnan ya dauka.
Daya daga cikin malaman, Adamu Popoi ya ce “An dade da sauke shi.”
Amma dakatarwar ta haifar da ce-ce-ku-ce da tsegunaguni a tsakanin ma’aikatan hukumar.