✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tawagar Gwamna Ortom ta yi hatsari a Binuwai

'Yan majalisar jihar guda biyu sun ji rauni a hatsarin.

Tawagar Gwamna Samuel Ortom na Jihar Binuwai ta yi hatsari a kauyen Utokon da ke Karamar Hukumar Ado ta jihar da safiyar wannan Juma’ar.

Ortom da tawagar tasa sun yi hatsarin ne a kan hanyarsu ta zuwa taron yakin neman zaben dan takarar Gwamnan Jihar na jam’iyyar PDP a Igumale, hedikwatar Ado.

Wakilinmu ya rawaito cewa, wata motar bas daga cikin tawagar ce ta kwace wa direbanta ta inda ta yi karon da wata mota a cikin jerin gwanon motocin, lamarin da ta zamanto sanadiyar hatsarin.

Wasu ‘yan majalisar jihar biyu da ke cikin tawagar na daga cikin wadanda suka ji rauni.

Ba tare da bata lokaci ba motar daukar mara lafiya ta kwashi wadanda suka ji rauni zuwa asibiti.