Wata kotun al’ada dake zamanta a jihar Ekiti ta datse igiyar wani aure mai shekaru 32 tsakanin Mista Oladipo Ogunleye da matarsa, Adeola Falade saboda kin biyan sadaki.
Shugaban kotun, Misis Yemisi Ojo ita ce ta yanke hukunci a ranar Laraba bisa zargin cewa mijin na kuma dukan matar tasa a kai a kai.
Alkalin ta ce a bayyane yake karara cewa babu aure a tsakanin mutanen biyu da suka kwashe tsawon wannan lokacin suna zaune tare da juna, inda nan take ta umarce su da kowa ya kama gabansa.
Ta ce, “Muna shawartar mai karar kan ya kara yaukaka dangantaka tsakaninsa da ‘ya’yansa guda biyar.
“Ina kuma shawartar matar kan ta rika basu dama su rika yin hutu a wajen mahaifinsu domin inganta dangantaka tsakaninsu, wanda kuma shi zai ci gaba da biyan kudaden makarantarsu.
“Muna kuma shawartar tsoffin ma’auratan kan su ci gaba da zama lafiya, domin duk wanda ya saba umarnin kotun to lallai zai fuskanci fushinta,” inji alkalin.
Tun da farko dai Mista Oladipo wanda bakanike ne ya ce babu aure tsakaninsa da matar amma suna da ‘ya’ya biyar.
Ya kuma shaidawa kotun cewa a lokacin da suke zaune tare shine yake daukar dukkan nauyinsu, amma tun da matar ta tafi da su ya daina daukar nauyin.
To sai dai matar wacce ma’aikaciyar gwamnati ce ta musanta dukkan zarge-zargen da mijin ya yi mata.
A cewarta, “Mijin nawa yak an dake ni, yak an kuma yi min barazanar kora ta daga gidansa.”