Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Femi Gbajabiamila ya ce tattauanwa ce kadai zata magance tarin matsaloli da kalubalen da ke addabar Najeriya.
Ya bayyana haka ne ranar Asabar a sakonsa na taya murna kan ranar Dimokradiyya ta 2021.
- Rikici ya barke yayin gangamin APC a Kano
- Maniyyata 60,000 ne kacal za su yi Aikin Hajjin bana – Saudiyya
Kakakkin a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawunsa, Lanre Lasisi Najeriya ta fuskanci sauye-sauye da ci gaba ta bangarori da dama, musamman ta bangaren ayyukan raya kasa da kuma yancin fadin albarkacin baki tun bayan dawowarta kan tsarin mulkin Dimokradiyya a shekarar 1999.
Gbajabiamila ya kuma jinjinawa ’yan Najeriya wadanda ya ce sun bayar da gagarumar gudunmawa ga shugabanni a cikin shekaru 20 din da suka gabata, tare da yin kira gare su kan su ci gaba da bayar da hadin kan.
Ya ce kowacce kasa a duniya na fama da irin nata kalubalen, inda ya ce Najeriya ma ba a barta a baya ba.
Sai dai ya ce duk da haka, har yanzu tsarin mulkin Dimokradiyya shine zakaran gwajin-dafi a tsakanin kasashe.
Kakakin ya kuma ce tattauanwa ita ce hanya daya tilo wajen magance kowacce irin matsalar da ake fama da ita a kasa.