✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tattalin arzikin Najeriya ya kusa farfadowa – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karfafa wa ’yan Najeriya gwiwa cewa, nan ba da jimawa ba tattalin arzikin kasa zai farfado kuma za a fita…

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karfafa wa ’yan Najeriya gwiwa cewa, nan ba da jimawa ba tattalin arzikin kasa zai farfado kuma za a fita daga radadin matsin  tattalin arzikin da ake fuskanta a yanzu, inda Najeriya za ta kara zama bunkasasshiya kamar yadda take a baya. Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a ranar Talatar da ta gabata, a yayin yakin neman zaben Gwamna na Jam’iyyar APC a Jihar Edo. “Ina ba ku tabbacin cewa za mu fita daga wannan matsi na tattalin arziki ba da jimawa ba,” inji shi.
Shugaba Buhari ya kara da cewa: “Zuwa yanzu dai saura kadan mu shawo kan tashe-tashen hankula da suka addabe mu, don haka za mu ci gaba da kokarin ganin Najeriya ta sake bunkasa; za mu dawo muna alfahari da kasarmu, kamar yadda muke a baya.” Ya bayyana cewa Najeriya babbar kasa ce, wacce Allah Ya wadata da yawan jama’a da kuma albarkatun kasa. Ya ja hankalin mutane da wani kalami da ya taba furtawa shekara 30 da suka gabata, lokacin da yake Shugabancin kasa na soja cewa: “Ba mu da wata kasa da ta wuce Najeriya, don haka ya zame mana wajibi mu natsu a nan tare mu cece ta.” Ya ce wannan magana har yanzu tana nan kuma za ta yi tasiri.
“Duk inda ka shiga cikin duniya ba kamar kasarka. Za ka iya tsallake sahara, idan ka yi sa’a ba ka hallaka ba a teku amma da zarar ka sauka kasar da ka nufa, kalar fatarka ma kadai ta isa ta zame maka matsala a can, komai girman iliminka kuwa,” inji Buhari.
A yayin yakin neman zaben, ya yi kira ga al’ummar jihar su zabi dan takarar Jam’iyyar APC a zaben da za a fafata a gobe Asabar, domin ci gaba da aikin gina jihar da Gwamna mai barin gado ya faro. “Ina taya Obaseki murna, wanda kwararre ne shi, na goyi bayansa a gare ku, ku zabe shi domin ya ci gaba da aikin raya kasa. Kuna da mutane masu kima, don haka ku rike su da kyau, ku tabbatar cewa sun samu nasara.” Inji shi.