Kasafin kudi na shekaar bana (2016) ya gagari ‘yan Majalisun Tarayya yin aiki akai ne saboda a gurinsu ba irin wanda suka saba yi ba ne, wanda suka saba yi shi ne, ‘a kasafta a ba su abin da suke so, shugaban kasa da ministoci su je can su karata, duk abin da zai faru ya faru, lahira ko oho. Babu ruwansu da talaka sai zabe ya zo. Idan ba haka ba, ai shugaban kasa duk kasar ce mazabarsa, amma su wasu yankuna ne mazabunsu, kowanne ya san yawan mutanen da suke mazabarsa.
Sanatoci da wakilai na kowace jiha sun san yawan mutanen jiharsu da irin bukatunsu. Misali Jihar Kano da tafi kowace jiha yawan mutane ita ce cibiyar ciniki ta Afirka ta Yamma wacce aka sani da yin fatauci da rakuma zuwa inda Sahara take, kusan dukkan mu manoma ne, na damina da na rani, ga masana’antu kowanne iri.
Filin Jirgin sama na Kano shi ne na farko a Afirka ta Yamma, duk wadanda za su shigo daga ko’ina sai sun sauka a Kano sannan su je inda suke bukatar zuwa a nan Najeriya da sauran kasashen na Afirka ta Yamma. Wanda kamata ya yi duk sanatocin mu da wakilanmu susan haka, ta yadda za su tabbatar sun samo mana duk abin da muke bukata na hakkinmu yadda za mu ci gaba, kowa ya samu aikin yi ya dogara da kansa. Ba wai su jira shugaban kasa shi zai tsara musu duk abubuwan da suka kamata su tsara wa wadanda suke wakilta ba. Gazawarsu da yin haka yana nuna rashin dacewa da aikin da aka zabo su dominsa.
Don haka gara babu su, da abar su suna ta wawushe mana arzikin kasa da hadin kan barayin shugabanni.
Idan kasafin kudi na bana ya tsallake siradin ‘yan majalisa Allah ne kadai ya san ci gaban da za a samu a wannan shekarar bisa la’akari da kokarin gwamnatin tarayya na tottoshe kafofin satar kudin gwamnati. Idan aka yi nasarar toshewar ko da rabin kasafin bara ya wadatar a yi ayyuka masu yawa, tunda dama sace kudin ake yi. Balle kuma da aka nunka na baran sau daya da rabi (kasha dari da hamsin).
Tun farkon farawa an ji yadda ‘yan majalisun suka shugabantar da kansu ta hanyar satar doka da irin zarge-zargen da ya biyo baya akansu. Ga bincinken da aka fara akan Dala biliyan biyu da miliyan 200. kafin a zo kan $20bil. na man fetur da $16bil. na wutar lantarki da $8bil. na Foreign Reserbe da Abacha Loot da $12.2bil. na lokacin yakin Tekun Fasha da £6.4bil na JMB London da sauransu. Ba’a san yawan mutanen da barayin shugabannin suka dasa a kowane bangare na gwamnati ba, musamman majalisun tarayya da gwamnonin jihohi. Bincike ne zai tabbatar da yawan su da yawan barnar da suka yi.
Ya kamata a bincika a gano su waye suka shayar da matasa ababen sa maye a dauki matakin da ya kamata don magance duk musifun da suke haifarwa ga al’umma. A dauki matakin gyara duk wata matsala, a hukunta duk wani mai laifi kamar yadda Allah ya yi umarni.
Kasafin kudin 2016 yana dauke da kudin gina gidan Mataimakin Shugaban kasa, da na Shugaban Majalisar Dattijai, da na Kakakin Majalisar Wakilai, kamar yadda mai bai wa Shugaban kasa shawara kan harkokin Majalisar Wakilai ya fada a BBC ranar Juma’a 12/2/16 da daddare a shirin Ra’ayi Riga.
Iya sani na duk wadannan gidaje akwai su, sai dai idan sayar da su aka yi. Idan har sayar da su aka yi, al’ummar Najeriya muna bukatar a gaya mana nawa aka sayar da su? Suwa aka sayarwa? Ina kudin??? Bana goyon bayan a sake fitar da wasu kudin don sake gina wasu gidajen. Ko dai a yi amfani da kudin da aka sayar da na da – a gina wasu, ko kuma ko suwaye suka sayi na da – Gwamnati ta maida musu da kudin su, su dawo da Gidajen. Idan ba so ake yi a wayi gari an sayar da Gidan Shugaban kasa ba!
Abdulkarim Daiyabu, Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya (MOJIN)
08060116666, 08023106666
Tattalin arziki ba ya ginuwa da kudin sata!
Kasafin kudi na shekaar bana (2016) ya gagari ‘yan Majalisun Tarayya yin aiki akai ne saboda a gurinsu ba irin wanda suka saba yi ba…