✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tattaki addini ne a wajen mu ‘Yan Shi’a – Malam Yakubu

‘Yan kungiyar nan ta ‘Yan-uwa musulmi wadda aka fi sani da sunan Shi’a, wadda gwamnati ta haramta wa yin tattaki, sun ce yin tattaki addini…

‘Yan kungiyar nan ta ‘Yan-uwa musulmi wadda aka fi sani da sunan Shi’a, wadda gwamnati ta haramta wa yin tattaki, sun ce yin tattaki addini ne a wajen su.

Mukaddashin shugaban kungiyar na kasa Malam Yakubu Yahaya Katsina, ne ya furta hakan a yau Asabar a wajen taron da suka yi na ranar kwanaki 40.

Malamin ya ce, suna yi ne domin tuna yadda aka ja ahalin gidan Manzo tun daga garin Kufa har zuwa Damaskas. Wannan tafiya sun yi ta a kasa a cikin kwanaki 40, wannan ne yasa in lokacin ya zo suke yin tattakin don tunawa tare da jin irin yadda suka ji a wancan lokacin.

Malamin har ila yau, ya ce, su basu fada da gwamnati, gwamnatin ce ke fada da su domin ta hana su aiwatar da duk wani aiki na ibadar da su suka fahimta akai, hatta da damar da dokar kasa ta basu.

Malam Yakubu ya ce, tuni su kofar su a bude take domin zama da gwamnati domin su san halin da suke ciki, tunda su sun fahimci gwamnatin. Da ya juya akan haramcin da gwamnati tayi masu na aiwatar da hidimomin su, sun shigar da kara a kotu domin neman masu hakkin su.

A karshe malamin ya ce, suna zaune da makwabtan su Iaflya sabanin yadda wasu ke hange.