✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsadar kayayyakin Najeriya iri daya ne da na sauran kasashe —Gwamnan CBN

Ya ce ba iya Najeriya ce take fuskantar matsalar ba

Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya ce babu bambanci tsakanin tashin farashin kayayyakin da ake fama da shi a kasar nan da na sauran kasashen duniya.

Ya ce hatta karin da aka samu na tashin farashin daga kaso 15.60 cikin 100 a watan Janairun 2022 zuwa kaso 20.77 a watan Satumba, iri daya ne da na sauran kasashen duniya.

Emefiele ya bayyana haka ne yayin taron cin abincin dare da Cibiyar Kula da Aikin Banki ta Najeriya (CIBN) ta shirya a Legas karo na 57.

Gwamnan bankin ya ce yadda farashin kayayyakin ya yi tashin gwauron zabo a watan Satumba ya biyo bayan yadda ya rika sauka a shekarar 2021, sakamakon manufofin da suka daidaita tattalin arziki a shekarar.

A cewarsa, “Har yanzu kayan abinci ne ke kan gaba wajen karuwar farashi. Hakan ya nuna karuwar da aka samu da kaso 23.34 a watan Satumba.

“Kazalika, a wannan tsakanin, ainihin farashin kayayyaki ya tashi daga kaso 13.87 zuwa kaso 17.60 a watan Janairu.

“Kari a kan ragowar dalilai na kasa da kasa, faduwar darajar Naira sakamakon yawan shigo da kaya daga ketare da kuma karuwar rikici tsakanin manoma da makiyaya a yankunan da suka fi noma abinci a nan Najeriya su ma sun dada ta’azzara abubuwa,” inji Emefiele.

Gwamnan na CBN ya kuma ce annobar COVID-19 da aka yi fama da ita a shekarar 2020 wacce duniya ta shafe kusan shekara 100 ba ta fuskanci matsin tattalin arziki irin nata ba ita ma ta taimaka wajen kara hauhawar farashin kayan.