✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tashin ‘bam’ a mashaya ya jikkata mutum 11 a Kogi

Wannan ne karo na biyu da hakan ke faruwa cikin kwana 18 a yankin

Rundunar ’yan sandan Jihar Kogi, ta battabar da fashewar wani abu da ake zargin bam ne a karo na biyu a yankin Kabba a ranar Lahadin da ta gabata.

Kakakin Rundunar a Jihar, SP William Ovye-Aya ne ya bayyana hakan, inda ya ce fashewar ta auku ne da misalin karfe 9:15 na daren Lahadin.

Sai dai jami’in ba yi karin bayani a kan yanayin fashewar ba, da kuma wadanda suka jikkata a ibtila’in.

Sai dai, Hukumar Babban Asibitin Kabba ta ce, ta karbi mutum 11 da suka jikkata jim kadan bayan aukuwar fashewar.

“Jim kadan bayan aukuwar fashewar, an zo mana da mutum 11, ciki har da mamallakiyar mashayar da abin ya faru, domin yi musu magani,” kamar yadda babban jami’i a asibitin, Dokta Ibrahim Sule ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Litinin.

Hukumar asibitin ta ce, bayan da aka zo da mai mashayar, Misis Omofemi Oyehunwa, sun shigar da ita dakin yin hoto don duba ta.

Oyehunwa ta bayyana damuwa game da harin, tare da bayyana shi a matsayin abu mai munin gaske.

Ta kara da cewa, “Allah ne kadai ya ceci rayuwata daga harin.”

Shugaban kungiyar raya yankin Kabba, Emmanuel Ajibero, ya ce wannan shi ne karo na biyu da irin wannan harin ya faru a Kabba a tsakanin kwana 18.

Daga nan, ya yi kira ga gwamnati da ma hukumomin da lamarin ya shafa da su yi abin da ya dace domin hana aukuwar hakan a nan gaba.

(NAN)