✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tashar Buhari: Da N30 sai a kai ka har gida a Kano

Tashar wucin gadi da ke share wa fasinjoji da direbobi hawaye a Kano

Masu zuwa Katsina da ke bi ta layin France Road a birnin Kano sun saba ganin layin kananan motoci a-kori-kura masu daukar fasinja zuwa unguwannin Kurna, Rijiyar Lemo da Bachirawa a  wata tashar mota ta wucin gadi da ake kira Tashar Buhari.

Direbobin kananan motocin da ke jigila a tashar sun shaida wa Aminya cewa tashar ta samo sunanta na Tashar Buhari ne daga matsin tattalin arzikin da Najeriya ta shiga a lokacin Shugaba Buhari

Tashar Buhari ta fara aiki ne kimanin shekara hudu da suka gabata domin share hawayen mutanen da ba sa iya bin kudin tasi ko babur mai kafa uku, kasancewar gwamnatin jihar ba ta da motocin fasinja.

Kafin samuwar Tashar Buhari, wasu mutanen a kasa suke takawa su koma gida bayan sun gama harkokinsu a kasuwanni, saboda ba za su iya biyan kudin mota ba.

Amma bayan samuwar tashar, sai fasinjoji, yawancinsu dattijai da samari masu kananan sana’o’i a kassunanin na hawan ta zuwa gida ko kasuwa a kan N40 ko ma a kyauta.

Yadda aka kafa tashar

Direbobin tashar sun bayyana wa Aminiya cewa baya ga matsin tattalin arziki da ya samar da tashar, yawan al’ummar unguwar Kurna (wadda ake wa lakabi da China saboda yawan jama’arta) ma na sa mutane hawa motocin.

Shugaban direbobin, Malam Mani, ya ce sun kafa tashar ce domin saukaka wa fasinjoji marasa hali yadda za su je su yi harkokinsu na neman halaliyarsu.

Malam Mani wanda ya shi ma direban a-kori-kurar ce a tashar kafin ya rasa motarsa ya ce shi ne ya yi ta ba wa abokansa baki kan su zo tashar su rika taimakawa.

“Samuwar Tashar Buhari ta saukaka wa mutane hanyar zuwa wuraren da suke son zuwa a kan lokaci kuma cikin sauki.

Wasu fasinjoji a bayan motar Tashar Buhari

Suna taimaka wa mutane

“Mutane da yawa ba sa iya biyan kudin mota N100, wasu ba su ma da ita, sai dai su taka a kasa zuwa Kurna.

“Amma idan ka zo nan, duk yadda aka yi za ka samu a kai ka gida, idan ma ba ka kudin mota za mu roki direbobinmu su taimaka maka.

“Ba mu da direbobi na din-din-din da ke daukar fasinja a nan. Sai direbobin sun gama manyan ayyukansu sannan suke zuwa nan su dauki mutane.

“Muna karbar N40 a kan kowane mutum daya kuma motocin na daukar mutum 15 zuwa 20,” inji shi.

Malam Mani ya ce direbobin ba sa biyan ko sisi saboda taimakon mutane suke yi su samu su koma gida.

Wani fasinja, Malam Lawan, ya ce yakan taka ne ya je kasuwa duk ranar da ba shi da kudi, “Amma da zuwan Tashar Buhari, yanzu a N30 kacal ma sai a kai ni gida.

“Wahalar da aka shiga a lokacin gwamnatin nan ne ya kawo hakan. Da can mukan samu kudi komai kankantarsa, amma yanzu kana iya zuwa har ka tashi baka samu ko sule ba.

“Gaskiya suna taimakawa domin harkar kasuwancin yanzu ta sauya, sai a hankali,” inji shi.

Matsalar zuwa Kurna

Sani Salisu Mai Jama’a, wani fasinja ne da wakilinmu ya gani a daura da Tashar Buhari.

Ya ce duk da cewa ba motocin tashar yake jira ba, amma idan ya rasa babur mai kafa uku zuwa Kurna, to sai zai hau motar Tashar Buhari.

Ya ce talauci da yawan al’ummar Kurna su ne manyan dalilan da suka sa ake hawa motocin kuma fasinjoji ne da kansu suka rada wa tashar sunan Tashar Buhari.

“Wani lokaci ba rashin kudi ba ne, amma al’ummar Kurna na da matukar yawa kuma koyaushe akwai cunkoson ababen hawa a can; ga shi wasu masu baburan ba sa zuwa can shi ya sa matsalar ta karu.”

Hadin hawa motar Tashar Buhari

Sani ya ci gaba da da cewa ya ce hawa motocin na da hadari domin barayi da ’yan sane kan yi amfani da damar wajen raba mutane da kayansu.

“Na san wani fasinjan da ya hau irin motocin da N70,000 a aljihunsa amma aka sace.

“Ya ki biyan N500 ya dauki shatar babur mai kafa uku ya tsira da kudinsa. Wannan ai matsolanci ne.

“Na kuma taba ganin wata daga cikin motocin da ana cikin tafiya ta bude da fasinjoji, wanda hakan ya yi sanadiyyar rasa rai bayan motar da ke bayanta ta bi ta kan fasinjan da ya fado,” inji Sani.

Zargin ganganci

Ya kuma zargi direbobin da ganganci saboda a cewarsa, ba sa tsayawa fasinjoji su sauka kafin su wuce, sai dai su kawai rage gudu fasinja ya diro su kuma su fizgi mota su wuce.

Sai dai direbobin sun musanta zargin inda suka ce fasinjojin ne da kansu suke yin tsalle su sauka da zarar direba ya fara shirin tsayawa, kafin ma mota ta gama tsayawa.

Rage wa direbobi zafe

Ana ganin Tsahar Buhari a matsayin wata hanya ta rage matsin aljihun da direbobi ke fuskanta.

Yawancinsu da ke yin wasu ayyukan sun ce idan suka je tashar da yamma sukan samu kudin sayen mai ko na hidimar iyalansu.

Daya daga cikin direbobin, Jamilu Muhammad, ya ce, “A nan nake samun kudin sayen biredi, da gawayi da na saya wa yara alawa.

“Ina aiki a Kasuwar Kofar Ruwa amma a Bachirawa nake da zaune da iyalina.

“Idan yamma ta yi nan nake zuwa in dauki fasinja, in samu N700 zuwa N800. Haka ma da safe, muna daukar mutane daga Rijayar Lemo mu kawo su nan”.