kungiyar da’awa da ayyukan jinkai ta mata mai suna kismud Da’awa da ke Abuja ta shirya taron karshen shekara tare da wa’azi ga mata mai taken: ‘Ya ku wadanda kuka yi imani’, inda aka gabatar da laccoci a kan matakan kyautata imani da kuma tsare shi.
An gudanar da taron a babban dakin taro na masallacin kasa da ke Abuja, inda ya samu halarcin dalibai daga rukunin makarantun Nurul Huda Islamiyya na kungiyar da sauran mata ma’aikata daga bangarori daban-daban da ke Abuja.
Babban bako mai jawabi, Ustaz Tamim Yusuf ya yi wa’azi a kan Imani da rabe-rabensa, inda ya kalubalanci al’ummar Musulmi da su nemi ilimi don inganta imaninsu da kuma kare shi.
Ya ce imani na karuwa da raguwa gwargwadon ayyukan mutum, kuma aikata abu guda ko furta shi ka iya raba mutum da shi. “Imani ba gado ba ne, ko nasaba, ko sala, ko abun saya, idan haka ne da dan Annabi Nuhu (AS), ko mahaifin Annabi (SAW), ko Larabawa, ko karuna sun mallake shi, saboda kusancinsu da masu shi.” Inji shi.
A jawabin Shugabar taron, Hajiya A’isha Umar Yusuf, wadda ita ce Editar farko ta jaridar Aminiya a kamfanin jaridun Trust, ta ce tarbiyyantar da iyali da mata ke jagoranta, ba zai samu kyakkyawar nasara ba sai da goyon bayan maza, saboda haka sai ta bukaci mazaje su guji zama ’yan amshin shatan ’ya’yansu a kan duk abin da suka ce suna so ko suka sa a gaba.
Hajiya A’isha ta kuma yaba da ayyukan da kungiyar kismud Da’awa ke gudanarwa, wadanda suka hada da kafa makarantu 7 na Nurul Huda a halin yanzu da gabatar da wa’azuzzuka da daukar nauyin sanya wa’azi a gidan rediyo da daukar nauyin karatun marayu da ciyarwa a lokacin Ramadan a karkara, sai kuma dinka sutura ga mabukata a lokacin bikin Sallah. Don haka ta bukaci a rika tallafa wa kungiyar da kudi, don ci gaba da aiwatar da su.
Sauran wadanda suka gabatar da wa’azi sun hada da Dokta Sa’id Abubakar Sibawaihi, shugaban sashen Larabci na Kwalejin Ilimi (COE) na Abuja da ke Zuba. Sai kuma Ustaz Shehu Ibrahim da ya yi addu’a ta musamman don kubutar da ’yan matan makarantar Chibok da aka yi garkuwa da su da kuma samun mafita a sakamakon kashe-kashen da ake yi a sassa daban-daban na kasar nan.
Bako na musamman, tsohon Ministan Abuja, Dokta Aliyu Umar Modibbo, wanda bai samu zuwa ba ya aiko da sakon taimako, kamar yadda ita ma Uwar taron, Hajiya Hauwa Abdullahi Idris uwargidan Ministan Sufuri ta aiko da nata taimakon.
Shugabar kungiyar kismud Da’awa da rukunin Makarantun Nurul Huda, Malama Halima Sa’id ta gabatar da jawabin godiya sannan ta bukaci mata su ci gaba da neman ilimin addini da na boko don samar da tarbiyya tagari ga iyalansu.
Taron kismud Da’awa: An bukaci mata su nemi ilimi
kungiyar da’awa da ayyukan jinkai ta mata mai suna kismud Da’awa da ke Abuja ta shirya taron karshen shekara tare da wa’azi ga mata mai…