✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taron kasa: Mu yafe wa juna

Edita ka ba ni dama in yi tsokaci kan taron kasa, a cikin jaridar Aminiya mai albarka. Mahalatta wannan taro a dubi Allah, a tattauna…

Edita ka ba ni dama in yi tsokaci kan taron kasa, a cikin jaridar Aminiya mai albarka. Mahalatta wannan taro a dubi Allah, a tattauna al’amuran da za su zama masu amfani9 ga al’ummar kasa. Mu talaka kuwa, sai mu ci gaba da addu’ar neman dace. Allah Ya sa taron kasa ya zama tafarkin warware dumbin matsalolin da suka damu kasa. Taron ya zama dalilin da za mu yafe wa juna, mu bar gaba da jin haushin juna; ya zama silar warware dabaibayin da ya yi tarnaki ga hadin kan kasa. A bunkasa masana’antu da kasuwanci da noma, a samar wa matasa aikin yi, tare da daukaka ilimi. Wadannan su ne amnufofin da suka dace a tattauna a wajen taron kasa, ta yadda tarayyar Najeriya za ta ci gaba da dorewa a matsayin dunkulalliyar kasa guda. Daga Amiru Isa Bakori 08075959086

Sakonnin waya

Ga Gwamnan Shema
Aminiya a isar da sakona ga Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Ibrahim Shehu Shema, Sarkin Yakin Hausa. Don Allah a daure ka sanya mana laina a hanyar Maska kafin ka sauka. Muna godiya. Daga Salisu Sabi’u dan adawa, Maska Loko 08180188477.

Jinjina ga Gwamnan Gombe
Aminiya ku ba ni dama in isar da sakon jinjinata ga Gwamnan Gombe, wato Talba a kan taimaka wa mahajjatan Gombe da kudi a Makka, har sau biyu. Allah Ya saka da alheri. Amin. Daga Alhaji Kankat Gombe 07085604839.

Kira ga Kawu Sumaila
Edita barka da aiki, ya aka ji da mu? Ina son ka ba ni dama in yi kira ga Kawu Sumaila Bakin Ganga, cewa da ilimi da mulki duk na Allah ne, kana nuna wa duniya cewa kai mai ilimi ne, amma ba ka amfani da shi, sai a siyasa kawai. Da za ka koma ga Allah kamar yadda Kwankwaso ya yi watakila ka dace. Daga Ali Fancy Garko a Kano 08171748500.

Rabon taki a Jihar Kaduna
Assalamu alaikum zuwa Edita. Bayan haka ina so ka ba ni fili in mika kukana gami da raba taki, sai ga shi wanda ya cika fom, ba shi aka ba, sai wanda ya ba da kudi ba. Ka huta lafiya. Daga Zubairu Saminaka 08057027244.

Ga Sufeto Janar
Aminiya don Allah ku sanar da Sufeto Janar na ’Yan sanda MD Abubakar, yau shekara goma da rasuwar babanmu, har yanzu ba a ba mu hakkinmu ba, duk hanyar da ake bi, mun bi, amma har yanzu shiru muna cikin wani hali. Daga Iyalan Insifekta Zakari Ya’u Katsina 08170622330.

Murna ga Dawayya
Edita ina neman ka ba ni fili a Aminiya in taya hajiyar hajiyoyi murna mahajjatan bana mata murna, wato Rukayya Dawayya haihuwar da Allah yua bayar na smaun da namiji. Allah Ya raya mana cikin rayuwar Musulunci. Daga Nasirui Shehu Usman TS/Guruza titin Atiku Sakkwato 08094809068.

Balaraben Sarkin Zazzau
Salam. Edita don Allah ga isar min da jinjina ga Balaraben Sarki, Alhaji Dokta Shehu Idris, da fatan an yi sallah lafiya. Daga Aminu Sani Kaduna 08021454493.

Jami’ar Jihar Sakkwato
Salam Editan Aminiya ina taya mutanen jihar Sakkwato murnan kaddamar da jami’ar jihar, wadda mai girma Gwamna Dokta Aliyu Magatakarda Wammako zai kaddamar a karshen wannan wata na Oktoba. Wannan ci gaba ne ba, a’a, har da Arewa gaba ki daya. Daga Rabi’u B. Lawal Funtuwa 08153171016.

Ta’aziyyar Fadar Bege
Salam. Aminiya don Allah ki mika min gaisuwa ga matar Fadar Bege (Fakon Mafadi Allah). Allah Ya ba ta hakurin wannan babban rashi. Daga Ummi Mai Awara 070177865193.

Ga wakilin Bakori/danja
dan majalisar mai wakiltar Bakori/danja a Jihar Katsina, ka ce ka gina masallatai da Islamiyoyi, a kowace mazabar kansila, to kazoo ka nuna mana in dai ba a duniyar sama ka gina su ba. Daga Musa Unguwar Maiyasin, danja, Jihar Katsina 08155648155.

In talaka zai sa rayuwarsa?
Edita wai ina talaka zai sanya rayuwarsa ya ji dadi ne; shin laifinsa ko na masu mulki ne? In kun yi zana-zanga, a ce muku ’yan ta’adda, idan kun yi shiru a ce ’yan boko Haram ne. To da wacce za mu ji, ana sayen motar miliyan 255; talaka ya sayi mashin din dubu 30, sai a bishi a kama. Allah Sarki talaka! Allah Ya bi ma hakkinmu. Daga dan Barno K/Hausa Jigawa. 08105596618.

Aminiya ta zama ta Kano da Kaduna
Jaridar Aminiya ta zama ta ’yan Kano da Kaduna. Kada wanda ya sake turo mana ita Sakkwato, ba mu saya, gaskiya tunda in mun bada aiki ba a bugawa. Don haka Edita ka ji tsoron Allah, muma muna sayen jaridar ga, amma ba a yi muna adalci. Daga Aliyu Sani 08189185516.

Fatan alheri ga APC
Salam. Ina yi wa al’ummar Najeriya fatan alheri, musamman ’ya’yan jam’iyyar APC. Daga Isma’il Alkyabba Funtuwa 07039495283.

Kuka ga Gwamna Shettima
Ko Gwamna Shettima ya san cewa har yanzu an rike wa daliban Jihar Barno sakamakon jarabawa na WAEC da NECO? Aminiya don Allah ku isar min da kukana a madadin daliban Jihar Barno. Mai girma Gwamna ka biya kudin jarabawar. Daga Muhammad Njagole Abuja 08072365816.

Matsalar fyade
Aminiya ku ban dama in muika kukana a kan matsalar da ke damunmu ta yawaitar fyade ga amta. Wannan yana faruwa a sanadiyyar shigar tsiraici da matan kan yi da sunan kwalliya. Don haka ya kamata a ji tsoron Allah, a rika sanya sutura da tufafi na kamala. Allah Ya shiryar da mu, a bisa tafarki madaidaici. Daga Ibrahim KSD. 08031944943.

Gaisuwa ga  Aminiya
Ina mika sakon gaisuwata ga ma’aikatan Aminiya, kuma a kodayaushe ina tare da ku. Daga Abubakar Hassan Wakili Musa Mada. 07015406241.