✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taron kasa: Maitar Shugaban kasa ta bayyana

A bisa ga yadda aka tsara a jiya Alhamis shugaban taron kasa, kuma tsohon Babban Cif Jojin kasar nan Mai shari`a Idris Kutigi da wasu…

A bisa ga yadda aka tsara a jiya Alhamis shugaban taron kasa, kuma tsohon Babban Cif Jojin kasar nan Mai shari`a Idris Kutigi da wasu daga cikin jiga-jigan taron suka mika wa Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan cikakken rahotonsu, bayan karkare zaman taron da aka yi a ranar Alhamis 14-08-14. An dauki tsawon sama da watanni biyar ana guudanar da taron, sabanin watanni uku da aka kiyasta tun farko za a kammala taron da aka fara a ranar Litinin 17-03-14.
Taron, wanda shi ne na biyu irinsa a cikin wannan mulki na dimokuradiyya, bayan wanda tsohon Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya gudanar a shekarar 2005, da rana tsaka. Shi ma wannan din ka iya cewa da rana tsaka Shugaba Jonatahan ya wayi gari a cikin jawabinsa na zagayowar cikar kasar nan da samun `yancin kai a ranar 1 ga watan Oktoban bara, ya bada shelar lallai za a yi wannan taro, duk kuwa da irin adawarsa a baya da ya nuna akan rashin dacewar irin wannan taro. Ba ma shugaban kasa ba, hatta `yan Majalisun Dokoki na kasa sun yi watsi da wannan taro, bisa ga abin da suka kira rashin dacewarsa, suka kuma hana shugaban kasa kudin da zai gudanar da taron, kudin da a farko aka kiyasata sun haura Naira biliyan bakwai.
Ba wai `yan Majalisun Dokoki na kasa ba suka nuna adawa da taron hatta babbar jam`iyyar adawa ta APC, da wasu daga cikin gwamnoninta, musamman na shiyyar Kudu maso Yamma sun ja daga akan ba su, ba tura wakilai taron. Yayin da wasu `yan kasa suka rika bayyana ra `ayin cewa kamata ya yi a gudanar da taron a zaman taro mai cikakken iko, wato ma`ana dukkan wani zababbe tun daga kan Kansila na karamar Hukuma har ya zuwa kan shugaban kasa kowa ya sauka a ba taron ikon tafiyar da kasa, har sai an kammala, amma dai haka ba ta samu ba. Kai karewa ma da karau kusan dukkan gwamnonin jam`iyyar adawa ta APC da suka yi bazanar kaurace wa taron, sai ga su, bayan tura wakilai da suka yi, wasu har tallafi ta fannoni da dama suka bai wa wakilansu, baya ga cikakkiyar manufar bai daya don shiyyoyinsu da suka ba su.
Don ya kawar da duk wani shakku daga zukatan `yan kasa da wakilan taron, a cikin jawabinsa na kaddamarwa, shugaban kasa ya gargadi wakilan da lallai su kaurace wa tattaunawa akan dukkan batutuwan da suka jibanci ko wadanda za su kawo rura wutar kabilanci ko jinsi ko yanki da son zuciya, bare kuma zargin juna da makamantansu. A takaice ya nemi Wakilan da su sa kishin kasa da sadaukarwa, don ci gaban kasar nan da al`ummarta. Shugaba Jonathan, ya yi amfani da wannan dama wajen mayar da martani ga wasu `yan kasa da suke zargin yana da wata manufa ta kashin kansa da yake so ya cimmawa a wannan taro. A nan sai ya bada amsa da cewa “Babban manufarmu ta kirkiro taron ba ta wuce kishin kasar da muke da shi ba,” in ji Shugaba Jonathan.
Amma sai ga shi tun daga farko fara taron har aka kammala shi, an ta zama ne cikin rashin amincewa juna, musamman tsakanin wakilan Arewa a gefe daya da na sauran wakilan  shiyoyin Kudu maso Yamma da na Kudu maso Kudu da na Kudu maso Gabas da wasu daga cikin na tsakiyar kasar (`yan Arewa da suke kiran kansu `yan midil belt).
Dama babban zargin da ake yi wa taron shi ne Shugaba Jonathan yana son ya yi “TAZARCE,” ko ta halin kaka da yadda zai buda wa `yan yankinsa masu arzikin man fetur kafar da za su kara samun kudin shigar da ake ba su daga kashi 13 cikin 100, daga arzikin man fetur da batutuwa da suka jibanci soke Majalisun kananan Hukumomi da daina ba su kaso daga kudin arzikin kasa da kirkiro `yan sandan jihohi da makamantan batuwa da sai an iya gyaran kundin tsarin mulkin da ake aiki da shi yanzu ko kuma wani sabo kana za su iya tabbata.
Iallai kuwa! ana tsakiyar gudanar da taron wasu daga cikin wakilan Arewa suka yi kuruwar cewa ana kokarin cusa wani sabon kundin tsarin mulki ga wakilan taron, bayan `ya`yar wannan jaridar da ake bugawa kullum-kullum Daily Trust ta ranar 30-06-14, ta bankado wani rahoto da ake zargin cewa akwai wani Kundi da yake yawo tsakanin wakilan taron, wanda ake so a tabbatar da shi a zaman sabon Kundin tsarin mulkin kasa na shekarar 2014, da sunan mahalarta taron suka rubuta shi. Amma tun a wancan lokacin shugaban taron Mai shari`a Kutigi ya nemi ganin Kundin, wanda bayan an mika masa kofensa, sai ya ce taro ba ya da masaniyar wannan Kundi, kuma koda ya zo gaban taro, to kuwa taro zai yi watsi da shi, a haka aka ci gaba da taro tamfar magana ta mutu murus.
Sai ga shi dawowar da aka yi a ranar 11-08-14, don karkare zaman taron, daga cikin kundaye uku da aka bai wa wakilan taron, daya sabon Kundin tsarin mulkin ne da aka dade ana zargin akwai shi, yayin da sauran biyu suke kunshe da bayanan taron gaba dayansa.
Bayan hayaniya ta yi hayaniya, wannan zama da aka dage da sunan a dawo jibi Laraba, shugaban taron Mai shari`a Kutigi ya yi taron sirri da Wakilan shiyya-shiyya, inda ya shaida masu cewa bisa ga umurnin shugaban kasa sakatariyar shirya taron ta shirya wannan daftarin sabon tsarin mulki, kuma ake neman taron ya amince da shi.
Lokacin da wasu daga cikin wakilan shiyya-shiyyar suka matsa wa Mai shari`a Kutigi da tambayoyi akan ko ya san taron ba shi da iznin ya rubuta sabon daftarin tsarin mulkin kuma dadin dadawa, ba daya daga cikin Kwamitocin taron20, da ya kawo rahotonsa da ya rubuta sabon tsarin mulki? Sai mai shari`a Kutigi da aka ruwaito cewa a cikin fushi yake a duk tsawon ganawar, ya ce  shi fa shugaban kasa ya umurce shi da yayi haka, kuma ba wani wakili da zai yi ma shi wata barazana, sannan ya kara da cewa wakilan Arewa da suka zake akan tuhumar tasa su kwan da sanin cewa koda kaurace wa taron za su yi ba su da rinjaye da za su canja kudurorin da aka cimmawa.
Kai! Ka ji mai karatu Mai shari`a Kutigi daya daga cikin tsofaffin Arewa (don ba ka kira shi dattijo ba yanzu), da ya kai kololuwar zama Babban Cif Jojin kasar nan bayan share shekaru aruru yana aikin da ake ganin ya gama lafiya, yanzu ga shi akan wannan babban aikin ceton kasa zai yi karkon kifi.
Taro dai ya kare, an kuma amince a sauya sunan wancan Kundin tsarin mulki daga “Kundin tsarin mulkin 2014” ya zuwa “Daftarin gyare-gyaren Kundin tsarin mulkin 1999.”Taro kuma ya bada shawarar a mika wancan kundi da sauran batutuwa da tsarin mulki ya yi tanadinsu ga  Majalisun Dokoki na kasa da na jihohi don bin hanyar da ta dace wajen gyaransu. Da wannan ka iya cewa da sauran rina a kaba. Yunkurin ganin tabbatuwar “TAZARCE” daga shugaba Jonathan ba karewa ta yi ba, tunda bai samu biyan bukata daga Wakilan taron kasa ba, taron da tun kafin a fara shi wasu suka ce ba shi da amfani. To yanzu din ma ba hakura zai yi ba, don haka ya rage wa `yan Majalisun dokokina kasa da na jihohi su zuba idanu su tare “TAZARCEN”. Allah Ya taimaka.